Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Dan Majalisar APC a Jihar Benue

Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Dan Majalisar APC a Jihar Benue

  • Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan majalisan jihar Benue ta tabbatar da nasarar Philip Agbese na jam'iyyar APC
  • Kotun ta yi fatali da ƙararrakin da abokann takararsa na jam'iyyun PDP da LP suka shigar suna ƙaƙubalantar nasararsa
  • Lauyan Agbese ya nuna gamsuwarsa kan hukuncin da kotun ta yanke inda ya bayyana cewa ta yi adalci

Jihar Benue - Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan majalisar jihar Benue mai zamanta a birnin Makurdi, a ranar Asabar ta tabbatar da nasarar Philip Agbese, na jam'iyyar APC a kujerar ɗan majalisan Ado/Okpokwu/Ogbadibo.

Abokan takararsa na jam'iyyun Peoples Democratic Party da Labour Party, Aida Narth da Ralph Ogbodo, sun maka Agbese a kotu bayan nasarar da ya samu a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, cewar rahoton Daily Trust.

Kotu ta tabbatar da nasarar Philip Agbese
Kotu ta tabbatar da nasarar Philip Agbese na jam'iyyar APC Hoto: Philip Agbese
Asali: Facebook

Ƴan takarar a cikin ƙararrakin da suka shigar sun buƙaci kotun da ta soke nasarar Agbese a zaɓen da sauran wasu abubuwa.

Kara karanta wannan

Jigon APC Ya Bayyana Muhimmin Dalili 1 Da Yakamata Atiku/Peter Obi Su Amince Da Hukuncin Kotu

Kotu ta zartar da hukuncinta

Amma kotun ta yi hukuncin da ya tabbatar da nasarar Agbese, bisa dalilin cewa masu shigar da ƙarar sun kasa kare kararsu a gaban kotun yadda yakamata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai shari'a Emeka Zedi Dada, wanda ya yanke hukunci a shari'ar Aida da Agbese, ya bayyana cewa ƙarar da aka shigar akan wanda ake ƙara ba ta cancanta ba, saboda cire suna ba bisa ƙa'ida bai mai matsayin a shigar da ƙara ba, sannnan mai shigar da ƙarar ta kasa kawo hujjoji masu kyau.

Haka kuma, kotun a ƙarar Ogbodo na jam'iyyar LP, ta yi hukunci cewa ya kasa kawo hujjoji kan cewa ba a gudanar da zaɓen bisa doka ba wanda hakan ya saɓa sabuwar dokar zaɓe.

Da yake martani kan hukuncin, Adetunji Oso, lauyan Agbese, ya gaya wa manema labarai cewa an yi adalci inda ya tabbatar da cewa Agbese zai cigaba da gudanar da ayyukansa a matsayin zaɓaɓɓen ɗan majalisar Ado/Okpokwu/Ogbadibo.

Kara karanta wannan

"Peter Obi Ya Kusa Zama Shugaban Kasa": Babbar Malamar Addini Ta Fadi Wani Sabon Wahayi

Yankunan Da Za Su Amfana Da Mulkin Tinubu

A wani labarin na daban kuma, mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa dukkanin yankunan ƙasar nan za su amfana da ayyukan gwamnatin Shugaba Tinubu.

MaShettima ya kuma buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri kan halin matsin tattalin arziƙin da ake ciki a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng