Sunayen Duka Sanatoci da ‘Yan Majalisu 9 da Aka Tsige a Kotun Sauraron Karar Zabe

Sunayen Duka Sanatoci da ‘Yan Majalisu 9 da Aka Tsige a Kotun Sauraron Karar Zabe

  • Ana cigaba da gudanar da shari’o’i a kotun karar zabe, wasu sun kalubalanci nasarar abokan takararsu
  • Alkalan sauraron korafin zabe sun yi fatali da kararraki da yawa, amma wasu sun yi nasara a karar da su ka kai
  • Wadanda kotu ta raba da kujerunsu sun hada da Sanatoci da wasu daga cikin ‘yan majalisar wakilan tarayya

Abuja - Rahoton da aka samu a safiyar Asabar daga Daily Trust, ya tattaro shari’o’in karar zaben da su ka dauki hankali, aka tsige ‘yan majalisu masu-ci.

'Yan Majalisa
Abubakar Sadiku-Ohere, Mukhar Yerima, Amobi Ogah, Jibrin Isa Hoto: Amobi Oga, @Senator_JIE, Mukhar Umar Yerima, @SenAbuOhere
Asali: Twitter

1. Udende vs Suswam

A jihar Benuwai, kotu ta maida Sanata Gabriel Suswam na jam’iyyar PDP majalisa, hakan ya na nufin mai shari’a Ory Zik-Ikeorha ya tsige Emmanuel Udende.

2. Adoji ya doke Jibrin Isa

Kotun sauraron karar zaben ‘Yan majalisar tarayya sun ta ba Sanatan Kogi ta Gabas rashin gaskiya, ta karbe kujerar Sanatan na APC, ta umarci a sake shirya zabe.

Kara karanta wannan

Shari’ar Zabe: Abin da zai faru da PDP da LP idan sun tafi kotun koli – Gwamna Bello

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

3. …Wani ‘Dan Majalisar Kogi

Abubakar Sadiku-Ohere ya na cikin wadanda aka doke a kotun zabe. Natasha Akpoti-Uduaghan ta karbe wurin Sanatan APC, Sanata Sadiku-Ohere a jihar Kogi.

4. Sanatan Kudancin Delta

Da aka je kotun farko, jam’iyyar PDP ta yi galaba kan Sanatan Delta ta Kudu, Thomas Onowakpo, yanzu ana shirye-shiryen sake shirya zabe nan da Nuwamba.

‘Yan majalisar wakilai

5. NNPP za ta rasa Tarauni?

A Kano, Muktar Umar Yerima ne kadai ‘dan majalisar NNPP da zuwa yanzu kotu ta ba rashin gaskiya, ta maidawa Hafizu Kawu kujerarsa saboda takardar firamare.

6. Minista za ta koma Majalisa?

Karamar ministar kwadago, Nkiruka Onyejeocha za ta iya komawa majalisa a sakamakon doke Hon. Amobi Ogah a kotun zabe, babu mamaki za a daukaka kara.

7. Dawowar Elumelu

Hon. Ndudi Elumelu ya yi galaba a kan Ngozi Okolie domin ba ta da rajista a LP a lokacin zaben 2023, ta na cikin ‘yan majalisar da jam’iyyar LP za ta iya asara.

Kara karanta wannan

Mai Neman Karbe Kujerar NNPP Ya Kunyata, Alkali Ya Ce a Biya ‘Dan Majalisa N100, 000

8. Kujerar Ogunyemi a Majalisa

A Legas, Seyi Sowunmi ya karbe kujerarsa bayan ‘dan jam’iyyar LP ya shafe watanni a Abuja sai kotu ta ce Hon. Lanre Ogunyemi bai dace ya shiga takara ba.

9. PDP ta sha kashi a Bayelsa

An ji yadda kotun da ke zama a Yenagoa ta tsige Fred Agbedi daga majalisa a kan zargin Michael Bless Olomu na kin hadawa da kuri’u 26, 000 a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng