Kotun Zabe Ta Kwace Kujerar Sanata APC, Ta Bai Wa Jam'iyyar PDP a Benue

Kotun Zabe Ta Kwace Kujerar Sanata APC, Ta Bai Wa Jam'iyyar PDP a Benue

  • Kotun sauraron kararrakin zaɓen NASS ta ayyana Sanata Suswam na PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen Sanatan Benuwai ta Arewa Maso Gabas
  • Hukuncin da Kotun ta yanke ya kuma tsige Sanatan APC daga kujerarsa a majalisar dattawan Najeriya
  • An samu saɓani tsakanin alkalai uku na Kotun yayin da yanke hukunci, inda biyu suka bai wa Sanata Suswam nasara

Jihar Benue - Kotun sauraron kararrakin zaben 'yan majalisun tarayya mai zama a Makurdi, babban birnin jihar Benuwai ta yanke hukunci kan zaben Sanatan Benuwai ta Arewa maso Gabas.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa Kotun ta ayyana Sanata Gabriel Suswam na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓe a ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Sanata Gabriel Suswam na jam'iyyar PDP.
Kotun Zabe Ta Kwace Kujerar Sanata APC, Ta Bai Wa Jam'iyyar PDP a Benue Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Haka zalika Ƙotun ta tsige Sanata Emmanuel Udende na jam'iyyar APC daga kujerar mamba a majalisar dattawan Najeriya mai wakiltar Benuwai ta Arewa maso Gabas.

Kara karanta wannan

Shari’ar Zabe: Abin da zai faru da PDP da LP idan sun tafi kotun koli – Gwamna Bello

Kotun zaɓen NASS da ke Makurɗi ta yanke hukunci ne a zamanta na yau Jumu'a, 8 ga watan Satumba, 2023, wanda ya shafe sama da sa'o'i uku.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanata Suswan, mamban majalisar dattawa ta Tara ya sha kashi a ƙoƙarinsa na sake komawa majalisar a zaɓe da ya gabata a watan Fabrairu, Vanguard ta rahoto.

Sai dai ya garzaya kotu, yana mai cewa ba Udende ne ya samu rinjayen kuri'un da aka kada a zaben Sanatan mazabar Benuwai ta Arewa maso Gabas ba.

Yadda Alkalai suka samu saɓani a hukuncin

Kotun ta bayyana cewa ta gamsu da ƙorafin masu kara cewa sun cika duka sharuɗɗan doka, bisa haka ta ba su nasara a hukuncin da ta yanke.

Shugaban kwamitin alkalai uku na Kotun da kuma mamba ɗaya sun yanke hukuncin da ya bai wa Sanata Suswam da jam'iyyar PDP nasara.

Kara karanta wannan

Bayan Hukuncin Kotun Zaɓe, Ministan Abuja Ya Tona Muhimmin Abu Game da Zaɓen Shugaban Ƙasa 2023

Sai dai ɗaya daga cikin Alkalan, mai shari’a Umar Mohammed, ya yi hannun riga da hukuncin da sauran mambobin kwamitin biyu suka yanke, yana mai cewa mai shigar da kara ya gaza tabbatar da ƙorafinsa.

Kotun Zabe Ta Tsige Dan Majalisar Tarayya Na PDP

A wani rahoton na daban kuma Kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar Bayelsa ta yanke hukunci kan zaben mazabar tarayya ta Sagbama/Ekeremor.

Kotun zaben ta yi watsi da nasarar Hon. Fred Agbedi na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sannan ta soke zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262