Jam'iyyar PDP Ta Zargi Gwamnan Jihar Kebbi Da Salwantar Da Biliyan 20 A Iska
- Jam'iyyar PDP ta zargi gwamnan jihar Kebbi da salwanta r da makudan kudade a iska inda ba amfani
- Shugaban jam'iyyar PDP a jihar, Alhaji Usman Bello-Suru shi ya bayyana haka a yau Juma'a 8 ga watan Satumba a Birnin Kebbi
- Da ya ke martani kan korafin, sakataren yada labarai na gwamnan jihar, Ahmed Idris ya ce PDP na kishi ne saboda ci gaban da su ka kawo
Jihar Kebbi - Jam'iyyar PDP ta zargi gwamnatin jihar Kebbi da lalata Naira biliyan 20 a Iska cikin kwanaki 100 kacal.
Jam'iyyar na zargin gwamnatin da barnatar da makudan kudaden a cikin kwanaki dari kacal na sabuwar gwamnatin.
Shugaban jam'iyyar a jihar, Alhaji Usman Bello-Suru ya yi wannan zargin ne a yau Juma'a 8 ga watan Satumba a Birnin Kebbi.
Meye PDP ke zargin Gwamna Idris na Kebbi?
Har ila yau, gwamnatin jihar ta yi watsi da zargin da cewa 'yan jihar na jin dadin yadda ake mulkarsu, cewar Vanguard.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jam'iyyar PDP ta ce gwamnatin jihar ta kashe har Naira biliyan 20 wurin kawata Birnin Kebbi, The Guardian ta tattaro.
Sanarwar ta ce:
"Mutanen yankin Zuru na fama da matsalar hanya wanda Naira biliyan 7 kadai ta isa ta cire su a wannan damuwa.
"Ya tabbata gwamnatin jihar ta kashe fiye da Dala biyu wurin tafiye-tafiye yayin da mutane ke cikin wani hali."
Meye martanin gwamna idris kan korafin PDP?
Usman ya kara da cewa gwamnatin ta kuma kashe biliyoyin kudade wurin wasu ayyuka da ba su da amfani a Birnin Kebbi.
Yayin da ya ke martani, Ahmed Idris, sakataren yada labarai na Gwamnan jihar, Nasir Idris ya ce dukkan wadannan zarge-zarge ba su da makama.
Ya ce jam'iyyar PDP ta birkice ne kawai saboda irin ci gaban da gwamnatin APC ta samar ga al'ummar jihar.
Gwamna Idris na Kebbi ya tura tawaga Jamhuriyyar Benin
A wani labarin, Gwamnan jihar Kebbi, Kwamared Nasiru Idris, ya aike da tawaga zuwa jamhuriyar Benin domin kai daukin sako wasu ‘yan jihar 10 da aka kama.
Rahotanni sun tabbatar cewa jami'an tsaron Jamhuriyar Benin sun cafke mutanen su 10 'yan jihar Kebbi a Najeriya kana suka tsare su a Magarkama.
Asali: Legit.ng