Zaben Kogi: Tsohon Mataimakin Gwamna Ya Fice Daga Jam'iyyar PDP
- Rikicin jam'iyyar PDP a Kogi ya ɗauki sabon salo yayin da tsohon mataimakin gwamna ya fice daga jam'iyyar a hukumance
- Arc Abayomi Awoniyi, ya aike da takardar murabus dinsa daga PDP zuwa ga shugaban jam'iyyar na ƙaramar hukumar Mopamuro
- Alamu masu ƙarfi sun nuna cewa jigon siyasar na shirin sauya sheka zuwa APC mai mulki nan bada daɗewa ba
Kogi - Rikicin da ya ɓarke a jam'iyyar PDP reshen jihar Kogi ya buɗe sabon shafi jiya Alhamis, 7 ga watan Satumba, 2023.
Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kogi a inuwar jam'iyyar PDP, Arc Abayomi Awoniyi, ya fice daga jam'iyyar a hukumance.
Ya ce zai fice daga jam’iyyar ne bayan shafe shekaru 25 na aminci da sadaukar da kai da hidimtawa PDP, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.
Awoniyi wanda ya rike mukamin mataimakin tsohon Gwamna Idris Wada, ya mika takardar murabus din sa ne ga shugaban jam’iyyar PDP a karamar hukumar Mopamuro ta jihar Kogi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai bai bayyana wace jam'iyya zai koma ba a cikin wasiƙar, wacce ke ɗauke da kwanan watan 31 ga watan Agusta, 2023.
Duk da bai ambaci dalilinsa na barin jam'iyyar PDP ba amma ana tsammanin ficewarsa ba zata rasa nasaba da rashin gamsuwa da zaɓen fidda gwanin takarar gwamna ba.
Wace jam'iyya tsohon mataimakin gwamna zai koma?
Alamu masu ƙarfi sun nuna cewa tsohon mataimakin gwamnan na shirye-shiryen sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki nan ba da daɗewa ba.
Ya yi wa takardar take da, “Wasikar murabus daga jam’iyyar PDP” kuma ta shiga hannun manema labarai ne jiya Alhamis.
Vanguard ta rahoto wani sashin wasiƙar na cewa:
"Na rubuta wannan takarda ne domin sanar da murabus ɗina daga jam'iyyar PDP bayan kwashe shekaru 25 ina biyayya, sadaukarwa da hidima."
"Ina mika sakon godiyata ga duka 'ya'yan PDP a karamar hukumar Mopamuro da ke Kogi ta Yamma, da ɗaukacin jihar baki daya bisa goyon bayan da suka bani da hadin kai tsawon shekaru."
Shugaba Tinubu Ya Bayyana Tarihin Karatunsa a Jami'a
A wani rahoton na daban kuma Shugaba Bola Tinubu ya bayyana tarihinsa na karatu a lokacin da yake jami'a, inda ya ce shi hazikin dalibi ne.
Yayin da yake jawabi ga ‘yan Najeriya mazauna Indiya, shugaban ya faɗi yadda Deloitte ya horar da shi sannan ya shiga kamfanin Exxon Mobil.
Asali: Legit.ng