Ministan Abuja Wike Ya Fara Yunkurin Korar Atiku da Tambuwal Daga PDP
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar ya da gamu sabuwar matsala yayin da yake kokarin ɗaukaka kara zuwa Kotun koli
- Tsohon gwamnan Ribas, Nyesom Wike, ya yi kira ga NWC ya dakatar da Atiku, Tambuwal da makamantansu daga jam'iyar PDP
- Wike, ministan birnin tarayya Abuja ya yaba wa Alkalan Kotun zaɓe bisa babban aikin da suka yi na yanke hukunci
Abuja - Rikicin babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa PDP na neman dawo wa sabo awanni bayan Kotun sauraron ƙorafin zaben shugaban ƙasa ta tabbatar da nasarar Bola Tinubu.
Tsohon gwamnan jihar Ribas kuma Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya shata layin sabuwar rigima tsakaninsa da mambobin PDP masu goyon bayan Atiku Abubakar.
A wannan karon, Wike ya buƙaci kwamitin gudanarwa na PDP ta ƙasa (NWC) ya dakatar da Atiku, tsohon darakta janar na kwamitin kamfen shugaban ƙasa, Aminu Tambuwal da sauran masu mara musu baya.
Wike ya yi wannan kira na dakatar da jiga-jigan PDP ne yayin hira da gidan Talabijin na Channels, cikin shirin siyasa a yau ranar Alhamis.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya kuma yi fatali da kalaman tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP, Dele Momodu, inda ya bayyana cewa ba zai iya lashe zaɓe a ƙaramar hukumarsa ba.
Wike ya yaba da hukuncin Kotun zabe
Tsohon Gwamnan Jihar Ribas ya kuma yi amfani da wannan damar wajen yabawa Alkalan Kotun sauraron ƙarar zaben Shugaban kasa kan aikin da suka yi.
A cewarsa, hukuncin wanda ya tabbatar da nasarar shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya dogara ne akan ingantaccen hukunci ta fuskar fasaha da kuma sanin aiki.
A rahoton Vanguard, Wike ya ce:
"A akwatun zaɓe ake gane muradin 'yan Najeriya, taya jam'iyyar PDP zata ci zaɓe idan ka duba yanayin da ƙasa ke cikin wancan lokacin?"
Hukuncin Kotu: An Bayyana Wani Muhimmin Dalili Da Zai Sanya Shugaba Tinubu Ya Cigaba Da Nasara Akan Atiku Da Peter Obi
“Ku dubi wuraren da PDP ba ta samu nasara ba saboda girman kai, saboda kwadayi saboda rashin sanin ya kamata. Da PDP ta yi abinda ya dace watakila da wani zancen ake yanzu."
Matsalar Tsaro: "Muna Bukatar Addu'arku" Ministan Tsaro Ya Roki Yan Najeriya
A wani labarin kuma Ministan tsaron tarayya, Badaru Abubakar, ya roƙi 'yan Najeriya su taimaka masa da addu'a domin magance matsalar tsaro.
Badaru ya yi wannan kira ne yayin da ya karɓi bakuncin wakilan jiharsa ta Jigawa karkashin jagoranci Gwamna Malam Umar Namadi a ofishinsa da ke Abuja.
Asali: Legit.ng