Hukuncin Kotu: Hadamar Atiku Ce Ta Jawa Jam'iyyar PDP Rashin Nasara, VON DG

Hukuncin Kotu: Hadamar Atiku Ce Ta Jawa Jam'iyyar PDP Rashin Nasara, VON DG

  • Shugaban VON ya bayyana babban dalilin da ya sa PDP ta sha kashi a babban zaben 2023 da ya gabata
  • Osita Okechukwu ya ce Atiku yana da haɗama da kwaɗayin mulki domin da ya mara wa ɗan kudu baya da wataƙila yanzu wani zancen ake daban
  • A cewarsa, tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya yi wa PDP babbar illa wanda zai wahala ta farfaɗo nan kusa

FCT Abuja - Osita Okechukwu, Darakta Janar na gidan rediyon VON ya ce ya fahimci bakin cikin da 'yan adawa suka shiga kan hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa (PEPC) ta yanke.

Okechukwu, wanda kuma mamba ne a jam’iyyar APC mai mulki, ya faɗi haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar Ya Taya Shugaba Tinubu Murnar Samun Nasara a Kotu? Gaskiya Ta Bayyana

Daraktan VON da Atiku Abubakar.
Hukuncin Kotu: Hadamar Atiku Ce Ta Jawa Jam'iyyar PDP Rashin Nasara, VON DG Hoto: Osita Okechukwu, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

A cewarsa, jam'iyyar PDP ta samu kyakkyawar damar farfaɗowa a babban zaben 2023 amma kwaɗayi da haɗamar ɗan takararta, Atiku Abubakar, ne ya hana jam'iyyar samun nasara.

Okechukwu ya ce girman kan da Atiku ya nuna na goyon bayan Peter Obi ko wani ɗan takara daga kudancin Najeriya, shi ne asalin abinda ya tarwatsa jam'iyyar PDP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A rahoton Vanguard, ya ce:

"Atiku ya yi wa jam'iyyar PDP babbar illa wanda zai wahala ta murmure ta farfaɗo nan kusa."
“Da ace Atiku ya yi biyayya ga tsarin karɓa-karɓa, ya goyi bayan Peter Obi ko kuma wani dan takarar shugaban kasa na Kudu, da ba wannan zancen ake ba."
"Rigimar Wike ba zata faru ba, kuma duk ƙuri'un da ya tatttara a zaɓen zasu tafi ga PDP ne. Atiku ya ja wa PDP asarar kuri'u domin duk ƙuri'un da Peter Obi ya samu na PDP ne."

Kara karanta wannan

Shugaban Majalisar Dattawa Ya Magantu Kan Hukuncin da Kotun Zabe Ta Yanke, Ya Fada Wa Atiku da Obi Mafita

Mista Okechukwu ya ƙara da cewa Tinubu ya cancanci yabo saboda ceto tsarin karba-karba na shiyya-shiyya wanda ya tabbatar da daidaito, da adalci tsakanin arewa da kudu.

Hukuncin Ƙotu: Atiku Ya Musanta Rahoton Taya Shugaba Tinubu Murna

A wani rahoton kuma Atiku Abubakar ya musanta rahoton da ke yawo cewa ya tura saƙon taya murna ga shugaban ƙasa, Bola Tinubu bayan hukuncin Kotu.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya ce rahoton ƙarya ne kuma ba shi da tushe, yana mai cewa tuni ya umarci Lauyoyinsa su fara shirin ɗaukaka ƙara zuwa Kotun koli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262