Hukuncin Ƙotu: Atiku Ya Musanta Rahoton Taya Shugaba Tinubu Murna

Hukuncin Ƙotu: Atiku Ya Musanta Rahoton Taya Shugaba Tinubu Murna

  • Atiku Abubakar ya musanta rahoton da ke yawo cewa ya tura saƙon taya murna ga shugaban ƙasa, Bola Tinubu bayan hukuncin Kotu
  • Mai magana da yawun Wazirin Adamawa, Paul Ibe, ya ce labarin karya ne wanda masu yaɗa farfagandar Tinubu suka kirkira
  • Ibe ya jaddada cewa tuni Atiku ya umarci lauyoyinsa su wuce zuwa Kotun koli domin kalubalantar hukuncin Kotun zaɓe

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya musanta rahoton da ke yawo cewa ya taya shugaban ƙasa, Bola Tinubu, murnar nasarar da ya samu a Kotun zaɓe.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya ce rahoton ƙarya ne kuma ba shi da tushe, yana mai cewa tuni ya umarci Lauyoyinsa su fara shirin ɗaukaka ƙara zuwa Kotun koli.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar.
Hukuncin Ƙotu: Atiku Ya Musanta Rahoton Taya Shugaba Tinubu Murna Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Depositphotos

Atiku ya bayyana gaskiyar lamarin ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Paul Ibe, ya fitar, kamar yadda jaridar Vanguard ta tattaro.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Dau Zafi, Ya Yi Wa Kashim Shettima Zazzafan Martani Kan Batun Yi Masa Ritaya a Siyasa

Kakakin Atiku ya maida martani

Da yake martani kan saƙon taya murnan wanda aka jingina wa Atiku, Mista Ibe ya ce wannan magana karya ce kuma wani bangare ne na makircin masu neman tabbatar da murɗe muradin ‘yan Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A ruwayar Leadership, Paul Ibe ya ce:

"Atiku ba zai iya aminta da 'yn fashin zabe ba saboda yin hakan zai zama fyade ga burin ‘yan Najeriya da suka kwashe shekaru suna gwagwarmayar tabbatar da sahihin zaɓe."
"Idan sun gamsu cewa nasarar da suka samu tana da inganci, ina ganin ba buƙatar su tsaya suna yi wa yan adawa zagon ƙasa wajen taya su murna ta hanyar labaran karya."
"Meyasa mutum zai ƙagu sai a an tabbatar? Shin gaskiya tana bukatar a tantance ta? Me zai sa ku fitar da saƙon taya murna kuma ku jingina wa Atiku idan kun san kuna da gaskiya."

Kara karanta wannan

Hukuncin Kotu: An Bayyana Wani Muhimmin Dalili Da Zai Sanya Shugaba Tinubu Ya Cigaba Da Nasara Akan Atiku Da Peter Obi

"Sabanin labaran karya da masu yada farfagandar Tinubu ke yadawa, tuni Atiku ya bukaci lauyoyinsa da su garzaya zuwa kotun koli domin kalubalantar hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe."

Ya kuma bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ba zai yi ritaya ba, maimakon haka zai ci gaba da fafutukar kafa dimokuradiyya a kasar nan.

"Ku Amince da Hukuncin Ƙotu" Sanata Akpabio Ya Shawarci Atiku da Obi

A wani rahoton kuma Sanata Godswill Akpabio ya yi kira ga yan adawa da su rungumi hukuncin da kotun zabe ta yanke wanda ya tabbatar sa nasarar APC.

Shugaban Majalisar Dattawan ya bayyana cewa hukuncin ya kara tabbatar da abinda yan Najeriya suka zaba da wadanda nauyi ya hauɓkansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel