Masu Zanga Zanga a Kotun Zabe Sun Bukaci Atiku da Obi Su Hada Kai da Tinubu

Masu Zanga Zanga a Kotun Zabe Sun Bukaci Atiku da Obi Su Hada Kai da Tinubu

  • Wasu dandazon mutane sun gudanar da zanga-zanga a Kotun sauraron kararrakin zaben shugaban ƙasa mai zama a Abuja
  • Masu zanga-zangar karkashin kungiyar CGGCI sun buƙaci Atiku da Peter Obi su haɗa hannu da Tinubu wajen ciyar za ƙasar nan gaba
  • Wannan na zuwa ne bayan Kotun ta tabbatar da nasarar Bola Tinubu kuma ta kori ƙarar Atiku da Obi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Wata ƙungiyar fafutukar kafa shugabanci na gari (CGGCI) ta aike da saƙon buƙata ga manyan 'yan takarar shugaban ƙasa biyu, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP.

Kungiyar ta gudanar da zanga-zanga ranar Laraba a a kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa (PEPT) yayin da take zaman yanke hukunci kan karar da Atiku da Obi suka shigar na adawa da nasarar Tinubu.

Kara karanta wannan

Minista Ya Bayyana Muhimmin Abu 1 Da Shugaba Tinubu Zai Warware da Zaran Ya Dawo Daga Indiya

Masu zanga-zanga a Kotun sauraron ƙarar zaben shugaban ƙasa.
Masu Zanga Zanga a Kotun Zabe Sun Bukaci Atiku da Obi Su Hada Kai da Tinubu Hoto: thecable
Asali: UGC

Masu zanga-zanga sun nemi haɗin kan Aiku da Obi

Da yake hira da 'yan jarida yayin zanga-zangar, Okpokwu Ogenyi, kodinetan kungiyar, ya ce ya kamata masu shigar da kara su lura cewa ‘yan Najeriya sun zabi Tinubu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jaridar The Cable ta rahoto Mista Ogenyi na cewa:

"Abin da muke nanata wa shi ne wannan gwamnatin (ta shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu) tana maraba da Atiku, Obi da Kwankwaso su shigo su bada gudummuwa."
“Abin da muke so shi ne mu tabbatar da nasara da ci gaban Nijeriya wanda muke ganin za a samu a karkashin gwamnatin Shugaba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu."
“Ba kuskure ba ne kasancewar mu ‘yan Najeriya kuma Allah ya kawo Asiwaju domin ya 'yanto al'umma daga radadin talauci. Asiwaju ya zo da alƙawura da yawa kuma ya fara cika su."

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Shugaba Tinubu Ya Gana da Fitaccen Attajirin Duniya a Indiya, Bayanai Sun Fito

Shugaban ƙungiyar ya ƙara da cewa tuni shugaba Tinubu ya fara kokarin bunƙasa tattalin arziƙin kasar nam domin mutane su amfana.

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton yadda Kotun sauraron kararrakin zaben shugaban ƙasa ta tabbatar da nasarar Bola Tinubu bayan ta kori karar Atiku da Obi.

Yajin Aikin NLC Ya Kawo Tsaiko a Yanke Hukuncin Kotun Zabe a Jihar Ogun

A wani rahoton kuma An samu jinkiri a zaman Kotun sauraron kararrakin zaben 'yan majalisar tarayya mai zama a Kotun sakamakon yajin aikin NLC.

Shugabannin ƙungiyar ma'aikatan shari'a ta Najeriya (JUSUN) ne suka kulle kofar shiga Kotun Majistire mai zama a Isabo, Abeokuta, wurin da Kotun sauraron ƙarar zaɓen ke zama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262