Jam’iyyar NNPP Ta Sake Doke Abba Ganduje a Kotu a Karar Zaben ‘Dan Majalisa
- Umar Abdullahi Ganduje bai iya yin galaba a kan Sanusi Bature Dawakin Tofa a kotun zabe ba
- Kotu ta tabbatar da nasarar Jam’iyyar NNPP a mazabar Dawakin Tofa/Tofa/Rimin Gado a Kano
- Alkali ya ce Abba Ganduje biya tarar kudi ga ‘dan majalisar wakilan tarayya saboda bata lokaci
Kano - Kotun da ke sauraron korafin zaben 2023 ya yi watsi da karar da Umar Abdullahi Ganduje ya shigar a kan takarar da ya yi.
Injiniya Umar Abdullahi Ganduje ya sha kashi kamar yadda jam’iyyar NNPP ta doke shi a zaben bana da aka yi, Aminiya ta kawo rahoton.
‘Dan takaran na APC mai mulkin Najeriya ya na kalubalantar nasarar da Tijjani Abdulkadir Jobe ya samu a zaben majalisar tarayya.
Zaben Tofa/Tofa/Rimin Gado a Kano
NNPP ta lashe zaben ‘dan majalisa mai wakiltar Dawakin Tofa/Tofa/Rimin Gado, inda yaron tsohon gwamnan Kano ya zo na biyu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A yayin da aka saurari karar a ranar Talata, Alkalan kotun sun bayyana cewa babu hujjojin da za su gamsar da su har a ruguza zaben.
Lauyoyin da su ka shigar da kara ba su gabatar da hujjojin da za su ba kotun sauraron korafin damar ba jam’iyyar APC mai-ci nasara ba.
'Dan takaran APC zai biya N200, 000
Rahoton ya ce a karshe sai dai aka bukaci Umar Ganduje ya biya Tijjani Abdulkadir Jobe kudi har N200,000 saboda bata masa lokaci.
Watakila Injiniya Ganduje ya yi biyayya ga hukuncin korafin zaben ko kuma ya kai maganar zuwa gaba a babban kotun daukaka kara.
Tijjani Jobe wanda ya sauya-sheka daga jam’iyyar APC zuwa NNPP bayan ya samu matsala da Abdullahi Ganduje ya koma kujerarsa.
Legit.ng Hausa ta fahimci Sanusi Bature Dawakin Tofa ya yi harin kujerar kafin shigowar Jobe NNPP, sai ya hakura da takararsa.
A Mayun 2022, jam'iyyar APC ta ba Abba tikiti yayin da mahaifinsa yake gwamna.
Ganduje vs Jobe a zaben 2023
A farkon shekarar nan aka ji Umar Abdullahi Ganduje yana cikin wadanda jam’iyyar NNPP ta dankara da kasa a zaben Kano da aka shirya.
Yaron tsohon Gwamnan ya sha kashi a hannun ‘dan majalisarsa, Honarabul Abdulkadir Tijjani Jobe Ganduje wanda ya kora daga APC.
Asali: Legit.ng