NNPP Ta Kori Rabiu Kwankwaso Daga Jam’iyyar, Cikakken Bayani

NNPP Ta Kori Rabiu Kwankwaso Daga Jam’iyyar, Cikakken Bayani

  • Jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta kori da dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023, Sanata Rabiu Kwankwaso
  • An kori Kwankwaso ne bayan ya ki bayyana a gaban kwamitin ladabtarwa na jam'iyyar don amsa wasu tambayoyi
  • Ana zargin tsohon gwamnan na jihar Kano da cin dunduniyar jam'iyya tare da wawure kudaden jama'a

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Rahotanni sun kawo cewa an kori dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Sanata Rabiu Kwankaso, daga jam’iyyar.

Kamar yadda jarida The Nation ta rahoto, kwamitin zartarwar jam’iyyar na kasa (NEC) ne ya sanar da batun korar Sanata Kwankwaso.

An kori Kwankwaso daga NNPP
NNPP Ta Kori Rabiu Kwankwaso Daga Jam’iyyar, Cikakken Bayani Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

An tattaro cewa korar Kwankwaso ya zama dole bayan ya ki gurfana a gaban kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar.

Dalilin da yasa aka kori Kwankwaso

Kara karanta wannan

Jerin Kararrakin Zaben Da Aka Gudanar Tun Shekarar 1999 Da Sakamakon Da Aka Samu

Hakan ya biyo bayan dakatar da shi da shugabancin NNPP ya yi a lokacin babban taron jam’iyyar na kasa wanda aka yi a Lagas a karshen makon watan Agusta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An dakatar da shi ne saboda zargin yi wa jam'iyyar zagon kasa da kuma karkatar da kudaden jam’iyyar.

Jam'iyyar ta kafa kwamitin ladabtarwa wanda ya gayyaci Kwankwaso don ya kare kansa a kan zarge-zargen da ake masa. Dan takarar shugaban kasar ya ki gurfana a gaban kwamitin don haka aka kore shi daidai da tanadin kundin tsarin jam'iyyar.

An sake tabbatar da korar Kwankwaso a ranar Talata, 5 ga watan Satumba, a cikin wata sanarwa da mukaddashin shugaban NNPP na kasa, Mista Abdulsalam Abdulrasaq ya fitar.

Jaridar Vanguard ta nakalto Mista Abdulrazaq yana cewa:

"Kwamitin NEC ya yi wani taron gaggawa a ranar Juma'a, 1 ga watan Satumba, kuma ya yanke hukunci kamar haka:

Kara karanta wannan

Ahaf: Uba Sani ya kama lagon PDP, ya ce shaidun adawa sun nuna shi ya ci zabe

"Bayan kin bayyanan Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a gaban kwamitin ladabtarwa da ya zauna a ranar Alhamis, 31 ga watan Agusta bayan an gayyace shi a rubuce, an kore shi daga jam’iyyar NNPP nan take.
“Za a kai karar tsohon dan takarar shugaban kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso wuraren da suka dace domin amsa tambayoyi kan badakalar kudi da ta shafi almubazzaranci da dukiyar al’umma.”

"Kwankwaso Matsala Ne a Siyasa" Sabon Shugaban NNPP Na Shiyyar Kudu

A baya mun ji cewa sabon mataimakin shugaban jam'iyyar NNPP na shiyyar Kudu maso Yamma wanda aka zaɓa kwanan nan, Alhaji Wasiu Ajirotutu, ya caccaki tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso.

Sabon mataimakin shugaban jam'iyyar ya ayyana Kwankwaso, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar NNPP a zaben 2023 da mutum mai son kai da ɗaukar alhaki a siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

iiq_pixel