Jerin Kararrakin Zaben Da Aka Gudanar A Najeriya Tun 1999 Da Sakamakonsu
Tun bayan dawowar dimukradiyya a Najeria a 1999 ake ta faman shari’a bayan zabe inda ake daukar lokaci don neman hakki daga wadanda ake ganin sun tafka magudi.
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
A jiya Litinin 4 ga watan Satumba kotun sauraran kararrakin zabe ta saka ranar Laraba 6 ga watan Satumba a matsayin ranar yanke hukunci ta karshe.
‘Yan takarar shugaban kasa a jam’iyar PDP, Atiku Abubakar da na jam’iyyar Labour, Peter Obi sun shiga kotu da zargin cewa an tafka magudi a zaben shugaban kasa.
Bayan daukar lokaci mai tsawo ana shari’ar, a yanzu za a iya cewa ta zo karshe bayan saka ranar yanke hukunci.
‘Yan Najeriya na dakon wannan rana don ganin yadda hukuncin za ta kasance inda kowa ke fadin albarkacin bakinsa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Legit.ng Hausa ta jero muku kararrakin zabe da aka gudanar tun 1999 da yadda su ka kasance:
1.Obasanjo da Olu Falae – 1999
Chif Olusegun Obasanjo wanda ya lashe zabe a 1999 bayan dawowar dimukradiyya ya yi nasara a kotun zabe kan abokin hamayyarsa, Olu Falae.
2.Obasanjo da Buhari – 2003
A shekarar 2003 Obasanjo ya sake zarcewa kan kujerar shugaban kasa inda ya doke Muhammadu Buhari na jam’iyyar ANPP.
A wannan karon ma Obasanjo ya sake nasara kan Buhari bayan yanke hukuncin kotu.
3.Marigayi Yar’adua da Buhari – 2007
Muhammadu Buhari ya sake garzawa kotu inda ya ke kalubalantar zaben da aka gudanar.
A wannan karon har ila yau, Buhari ya sake rasa damar kwace mulki inda kotu ta bai wa Umaru Musa Yar’adua na jam’iyyar PDP nasara.
4.Jonathan da Buhari – 2011
A karo na uku, Buhari na jam’iyyar CPC ya kalubalanci zaben da aka gudanar inda ya sake rashin nasara bayan kotu ta tabbatar da Goodluck Jonathan na PDP wanda ya lashe zabe.
5.Buhari da Jonathan – 2015 (Babu kara)
A 2015 babu wanda ya kalubalanci zabe wanda Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ya samu nasara a zaben da aka gudanar, kamar yadda TheCable ta tattaro.
6.Buhari da Atiku – 2019
Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya garzaya kotu don neman a bi masa kadunsa, amma kotun ta tabbatar da Buhari a matsayin wanda ya lashe zabe.
7.Tinubu da Atiku, Peter Obi – 2023
Bayan sanar da Bola Tinubu wanda ya lashe zabe, Atiku na jam’iyyar PDP da Peter Obi na jam’iyyar Labour sun garzaya kotu kan kin amincewa da sakamakon zaben.
A yanzu ana jiran yanke hukunci a ranar Laraba 6 ga watan Satumba na wannan shekara.
Kotu Ta Saka Ranar Yanke Hukuncin Zaben Shugaban Kasa
Awani labarin, Kotu ta saka ranar Laraba 6 ga watan Satumba don yanke hukuncin kararrakin zabe.
'Yan takarar shugaban kasa daga jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar da na jam'iyyar Labour, Peter Obi na kalubalantar zaben shugaban kasa.
Asali: Legit.ng