Jam'iyyar PDP Ta Yi Martani Bayan Kotu Ta Sanya Ranar Yanke Hukuncin Karar Zaben Shugaban Kasa

Jam'iyyar PDP Ta Yi Martani Bayan Kotu Ta Sanya Ranar Yanke Hukuncin Karar Zaben Shugaban Kasa

  • Jam'iyyar PDP ta yi martani bayan kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta sanya ranar yanke hukunci
  • Kotun sauraron ƙararrakin ta sanya ranar Laraba, 6 ga watan Satumba a matsayin ranar da za ta yanke hukuncinta
  • Jam'iyyar PDP na daga cikin jam'iyyun da ke ƙalubalantar nasarar da Shugaba Tinubu ya samu a zaɓen 2023

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ta yi martani bayan kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta sanar da ranar da za ta yanke hukuncinta.

Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa ido ya koma kan kotun yayin da ƴan Najeriya da sauran ƴan ƙasashen waje ke zaman dakun hukuncin da kotun za ta yanke.

PDP ta yi martani kan lokacin yanke hukuncin karar zaben shugaban kasa
PDP ta nuna kwarin gwiwarta kan hukuncin da kotu za ta yanke Hoto: Atiku Abubakar, Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen dai ta fitar da ranar Laraba, 6 ga watan Satumba, a matsayin ranar da za ta sanar da hukuncinta kan ƙararrakin da ke ƙalubalantar nasarar Shugaba Tinubu.

Kara karanta wannan

Manya-manyan Bukatu 5 Da Peter Obi Ya Mikawa Kotu Kan Shari'arsa Da Bola Tinubu

"Muna jiran hukuncin kotu", PDP

Da take martani kan sanya ranar yanke hukuncin, jam'iyyar PDP ta yi rubutaua shafinta na X (wanda a baya aka sani da Twitter), inda take cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Yanzu ta tabbata: Kotun ɗaukaka ƙara ta sanya ranar Laraba, 6 ga watan Satumban 2023, domin yin hukunci kan ƙarar da babbar jam'iyyar mu @OfficialPDPNig, da ɗan takarar shugaban ƙasar mu a zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, @atiku kan haramtaccen bayyana @officialABAT na jam'iyyar @OfficialAPCNg a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
"Idanunmu sun koma kan ɓangaren shari'a yayin da ƴan Najeriya da sauran ƴan ƙasashen waje ke zaman dakun jiran hukuncin kotun."

PDP na neman a kwace nasarar Tinubu

A ƙarar da jam'iyyar PDP da ɗan takararta suka shigar a gaban kotun, suna neman kotun ta ƙwace nasarar da Shugaba Tinubu ya samu a zaɓen shugaban ƙasa na shekarae 2023.

Kara karanta wannan

Shari'ar Atiku Da Obi: Jerin Kararraki 3 Da Aka Shigar Kan Tinubu a Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓe

PDP da Atiku sun haƙiƙance cewa Shugaba Tinubu ba shi ne ya lashe zaɓen ba kamar yadda hukumar zaɓe mai zaman kanfa ta ƙasa (INEC) ta sanar.

'Yan Arewa Za Su Juya Baya Ga Tinubu

A wani labarin kuma, ƙungiyar Inyamurai ta Ohanaeze Ndigbo ta bayyana cewa Shugaba Tinubu ba zai jo da daɗi ba a wajen ƴan Arewa, idan kotu ta umarci a sauya zaɓe.

Ƙungiyar ta yi nuni da cewa ƴan Arewa masu yaba da kamun ludayin salon mulkin Shugaba Tinubu ba, inda su ke ganin yana fifita yankinsa na Yarbawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel