Wasu ‘Yan NNPP Sun Fasa Kwai, Za Su Binciki Su Kwankwaso a Kan Bacewar Naira Biliyan 1

Wasu ‘Yan NNPP Sun Fasa Kwai, Za Su Binciki Su Kwankwaso a Kan Bacewar Naira Biliyan 1

  • Rigimar cikin gidan New Nigeria Peoples Party ya jawo ana maganar binciken inda aka ka kudin fam
  • ‘Yan tawaren jam’iyyar hamayyar sun nuna za ayi bincike a kan mutanen Rabiu Musa Kwankwaso
  • Abdulsalam Abdulrasaq ya zargi ‘Yan bangaren Kwankwaso da rashin adalci da handame Naira Biliyan 1

Abuja - Wani bangare na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party a karkashin Major Agbo, zai binciki Rabiu Musa Kwankwaso da mutanensa a NNPP.

Daily Trust ta ce Major Agbo ya na zargin Rabiu Musa Kwankwaso da ‘yan bangarensa da karkatar da N1bn da jam’iyyar ta samu daga saida fam.

Jam’iyyar hamayyar ta NNPP ta samu kudi masu yawa a lokacin zaben 2023 da aka yi, sai dai yanzu rigimar cikin gida ya lullube ta da magoya baya.

Kwankwaso NNPP
Rabiu Kwankwaso bayan zaben 2023 Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

Abdulrasaq ya zana Kakakin 'Yan tawaren NNPP

Kara karanta wannan

Tsabagen Kiyayya Ya Jawo Mawaki Ya na Kiran Sojoji Su yi wa Tinubu Juyin Mulki

Sakataren yada labaran ‘yan taware a jam’iyyar, Abdulsalam Abdulrasaq, ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar bayan sun yi zama a sakatariyar kasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jawabin ya ce za a bi diddikin duk wasu kudi da aka zargin an batar tun daga 2022 zuwa yanzu.

“NNPP za ta yi bincike da kyau a kan yadda aka yi fatali da fiye da Naira biliyan daya da aka samu daga saida fam ga masu shirin takara daga Maris na 2022 zuwa yau.
Taron ya yanke shawarar a gayyato hukumomin tsaro su yi binciken asusun jam’iyyar da kyau da nufin samun bayani daga ’dan takarar shugaban kasa da tsohon shugaban jam’iyya wanda ya tafi a watan Maris 2023, shugaban rikon kwarya da aka tsige da kuma sakatare na kasa.

- Abdulsalam Abdulrasaq

Kara karanta wannan

Kaico: Akalla mutum 61 aka mayar marayu bayan harin da aka kai masallacin Kaduna

Karin zargi a kan Rabiu Kwankwaso

Jawabin kamar yadda Punch ta rahoto, ya ce binciken zai kara karfin gwiwar ‘yan jam’iyya, masu shirin shiga takara su iya fitar da kudi domin sayen fam.

Abdulrasaq ya kuma soki yadda aka kafa dakin bibiyar zaben sakamakon zaben 2023 a gidan wanda ya yi wa jam'iyyar NNPP takarar shugaban kasa a 2023.

An zargi jam’iyyar da rashin adalci wajen tsaida ‘yan takara, saboda haka za a kafa kwamiti da zai binciki Injiniya Buba Galadima wanda jigo ne a NNPP.

Kwankwaso yana nan a jam'iyya NNPP

Ana da labari shugaban NNPP na kasa, Kawu Ali ya raba gardamar rigimar gidan da ta barko masu, ya ce ba za a iya dakatar da Rabiu Kwankwaso ba.

Ladipo Johnson ya fitar da jawabi a madadin NWC, ya yi watsi da dakatarwar da aka yi wa Kwankwaso, yake cewa shi ne wanda ya fito da jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng