Betta Edu Ta Bayyana Tsare-tsaren Shugaba Tinubu a Kan Shirin N-Power
- Dakta Betta Edu, ministar harkokin jin ƙai da rage raɗaɗin talauci ta yi magana kan shirin N-Power a gwamnatin Tinubu
- Ta ce za a sake fasalin tsarin ta yadda wasu za su ƙara samun shiga, da kuma gyara tsarin biyan alawus
- Ministar ta tabbatar da cewa za su yi gyare-gyare don magance matsalolin da ake fuskanta wajen biyan alawus na aiki
FCT, Abuja - Dakta Betta Edu, ministar harkokin jin kai da rage radadin talauci, ta ce Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Bola Tinubu, za ta yi wa shirin N-Power sabbin sauye-sauye.
Ministar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da hadiminta Rasheed Zubair ya fitar a ranar Lahadi kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Tsare-tsaren Tinubu kan shirin N-Power
Dakta Betta Edu ta ce yanzu haka akwai shirye-shiryen da suke yi a ƙasa domin sake fasalin shirin na N-Power don bai wa ƙarin mutane damar shigowa daga ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta kuma ba da tabbacin cewa za su yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun magance matsalolin da ake fuskanta wajen biyan alawus na ma'aikatan na N-Power.
Haka nan kuma Dakta Betta Edu ta ce ma'aikatar ta su na shirin samar da cibiyoyi jin ƙai a ƙananan hukumomi 774 da ake da su a fadin Najeriya.
Tinubu zai yi yaki da talauci a Najeriya
A cewar Edu, gwamnatin Tinubu na shirin ganin ta rage yawan talauci da ake fama da shi a faɗin ƙasar, ta hanyar samar da ayyukan yi da dama kamar yadda Premium Times ta wallafa.
Ta ƙara da cewa akwai tsare-tsaren da shugaban ya zo da su da za a ga amfanin wasu daga ciki nan kusa, yayin da wasu kuma sai can gaba.
Betta Edu ta kuma bayyana cewa ma'aikatarta za ta tura jami'anta zuwa ƙananan hukumomin ƙasar nan domin tabbatar da cewa an raba kayayyakin tallafi yadda ya kamata.
'Yan N-Power sun nemi Tinubu ya kawo mu su ɗauki
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan koken da matasa masu hidimtawa ƙasa a ƙarƙashin shirin N-Power suka miƙa wurin shugaba Tinubu dangane da alawus ɗin wata-wata da ake ba su.
Matasan na N-Power rukunin C1 da C2 sun koka da cewa an share watanni aƙalla takwas ba tare da an tura mu su ko sisi a cikin asusun bankunansu ba.
Asali: Legit.ng