Tinubu Ya Umurci A Raba Gilashi Miliyan 5 Ga Yan Najeriya Masu Matsalar Ido
- Tinubu ya ce dole ya tsaya kai da fata don tabbatar da an kawar da lalurar gani a fadin Najeriya saboda hakan ya taba shafar shi
- Tinubu ya ce wannan alkawari ne da ya yi wa mahaifiyarsa biyo bayan lalurar gani da ta samu kafin a yi mata magani
- Shugaban ya bayyana haka ne a wata ziyara da Shugabancin Gidauniyar Peek Vision suka kai masa a ranar Juma'a 1 ga watan Satumba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Fadar Shugaban Kasa - Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar Juma'a, 1 ga watan Satumba ya amince da wani shiri da zai samar da gilasai sama da miliyan biyar ga yan Najeriya masu matsalar gani.
Mai magana da yawun Tinubu, Ajuri Ngelale, cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja ya ce Shugaban ya bada cikakken goyon baya kan wata hadin gwiwa tsakanin shirin kula da lafiyar ido na Hukumar Lafiyar Najeriya da Gidauniyar Peek Vision.
Gwamnatin Najeriya Ta Kawar Da Fargabar Juyin Mulki Yayin da Sojoji Suka Hambarar Da Gwamnati a Gabon Da Nijar
Ngelale ya ce Shugaban ya bayyana yadda ya san matsalar ido tun daga gida a matsayin babban dalilin goyon bayan shirin.
Tinubu ya dauki alkawari a madadin gwamnatin tarayya yayin ziyarar da Shugaban Gidauniyar Peek Vision kuma Mataimakin Shugaban Gidauniyar Catalyst Fund, Farfesa Andrews Bastawrous.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola Tinubu: Abin da yasa na mayar da hankali kan lafiyar ido
Tinubu ya ce:
"Zan iya tuna abin da ya faru da mahaifiyata. Lokacin bata da lafiya har ta kai bata gane ni. Na tsaya, aka yi mata magani aka bata gilashi."
"Abu na gaba da ta fada min shine: ina da kai, zaka iya daukar nauyi na. To sauran mata da yara da ke fama da irin wannan lalurar waye zai dau nauyin su?
"Daga nan na dauki alkawari zan dauki nauyin al'umma da yawa don duba su tare da yi musu aiki saboda wancan magana ta mahaifiyata da son ta ga wasu sun samu waraka.
"Mun samu nasarar ceto miliyoyin masu matsalar gani a Legas, kuma kana iya ganin yadda suke farin ciki a bayyane bayan dawo da ganinsu ta hanyar gilashi."
Da ya ke jadada muhimmancin inganta harkar lafiyar ido a Najeriya, Ngelale ya ce Tinubu ya nuna damuwarsa kan fiye da mutane miliyan 24 da ke fama da matsalolin ido daban-daban.
Gwamnatin Tinubu Ta Tura Wa Jihohi Biliyan 2 Maimakon Biliyan 5
A wani rahoton, Gwamnatin Tarayya ta tura wa kowace jiha naira biliyan 2 ne kacal daga cikin Naira biliyan 5 da ta amince za ta bai wa jihohi a matsayin tallafi domin rage tasirin cire tallafin man fetur.
Gwamnatin karƙashin jagorancin Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ta sakar wa kowace jiha naira biliyan 2 ne domin daƙile hauhawar farashin kayayyaki idan ta saki naira biliyan 5.
Asali: Legit.ng