Primate Elijah Ya Hasaso Juyin Mulki a Kasashen ECOWAS 2 Da Kuma Ƙasa 1 a Afrika Ta Tsakiya
- Primate Elijah Ayodele, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church ya hasaso juyin mulki a ƙarin wasu ƙasashen
- Ayodele ya ce ƙasashen ECOWAS biyu ne da wata ta Afrika ta Tsakiya ɗaya ce ya hangowa juyin mulki nan kusa
- Ya ce ƙasashen Kamaru da Togo ya hasaso a Afrika ta Yamma, wai Equatorial Guinea a Afrika ta Tsakiya
Primate Elijah Ayodele, na 'INRI Evangelical Spiritual Church', ya ce akwai yiwuwar shugabannin Afrika su fuskanci ƙaruwar juyin mulki a cikin kwanakin nan.
Ya bayyana hakan ne a cikin wani ɗan gajeren bidiyo da ya wallafa ranar Juma'a, 1 ga watan Satumba, a shafinsa na X.
Kashen Afrika da Ayodele ya ce za a yi juyin mulki
Ayodele ya bayyana cewa ƙasashen ECOWAS guda biyu ne ya hasasowa juyin mulki nan ba da jimawa ba. Kasashen su ne Kamaru da kuma ƙasar Togo.
Hadimin Atiku Ya Bukaci Wike Ya Rushe Fadar Shugaban Kasa, Barikin Soji Da Wasu Muhimman Wurare a Abuja
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Haka nan ya ƙara da cewa ƙasar Equatorial Guinea, wacce take a yankin Afrika ta Tsakiya na za ta fuskanci juyin mulki daga soji.
Wannan hasashe na Elijah Ayodele dai na zuwa ne a ƙasa da sa'o'i 72 da dakarun soji suka hamɓarar da gwamnatin farar hula ta ƙasar Gabon.
Ayodele ya ce babu wanda zai iya hana juyin mulkin faruwa
Juyin mulkin na Gabon ya biyo bayan wanda sojoji suka yi a jamhuriyar Nijar a ranar 26 ga watan Yuli, wanda ya sha suka daga ƙasashe.
Elijah Ayodele ya bayyana cewa akwai ƙarin ƙasashen da za a karɓe mulkinsu kuma babu wani abu da wani zai iya yi a kai.
Malamin cocin ya kuma yi zargin cewa shugaban ƙasar Togo na yunƙurin sauya kundin tsarin mulkin ƙasar ta yadda zai ci gaba da shugabanci har ya mutu.
Sai dai ya ce hakan ba zai haifar da ɗa mai ido ba domin kuwa zai janyo hayaniya inda daga nan ne kuma sojoji za su ƙwace ƙasar.
Ƙungiyar AU ta dakatar da Gabon daga cikin mambobinta
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan matakin da kungiyar tarayyar Afrika ta ɗauka kan ƙasar Gabon na dakatar da ita daga cikin mambobinta.
Hakan ya biyo bayan juyin mulkin da sojojin ƙasar suka yi wa gwamnatin farar hula ta a Ali Bongo a ranar Laraba da ta gabata.
Asali: Legit.ng