Ministan Tinubu, Keyamo, Ya Bada Umurnin Rushe Filin Jiragen Sama Na Legas, Ya Bada Dalili

Ministan Tinubu, Keyamo, Ya Bada Umurnin Rushe Filin Jiragen Sama Na Legas, Ya Bada Dalili

  • Sabon ministan Shugaba Bola Ahmed Tinubu na sufurin jiragen sama da cigaban samaniya, Festus Keyamo, ya ce a rushe wurin ajiye jiragen sama na Dominion da EAN da ke MMIA 2 a Legas
  • Ministan ya ce za a yi hakan ne domin shirin gyara da fadada filin tashin jiragen saman da ake shirin yi
  • Keyamo ya bada umurnin yayin da ya ke duba filin jiragen saman a ranar Alhamis, irinsa na farko tunda ya kama aiki a matsayin minista

Festus Keyamo, ministan sufurin jiragen sama ya bada umurnin rushe wuraren ajiye jiragen sama na EAN da ke fiilin tashin jirage na Murtala Mohammed ta Biyu (MMIA 2), da ke Legas. Ya ce a rushe su nan take.

A cewar Daily Independent, ministan ya ce rushewan zai bada daman a fadada filin sauka da tashin jiragen saman.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Dakatar Da Wasu Manyan Ayyuka 2 Da Buhari Ya Fara

Keyamo ya bada umurnin rushe filin jirgin sama a Legas.
Keyamo ya bada umurnin fadada filin jirgin sama na Legas. Hoto: Festus Keyamo, Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Keyamo ya yi korafi kan rashin tsafta a MMIA yayin ziyararsa

Keyamo ya bada umurnin ne a ranar Alhamis, 31 ga watan Agusta, a lokacin da ya ziyarci filin tashin jirage na Legas domin duba halin da ya ke ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan ya nuna bacin rai bisa yadda aka bar filin jirgin cikin kazanta. Ya bada umurnin a tsaftace wurin nan take.

Keyamo na daya daga cikin ministoci 45 da Shugaba Bola Tinubu ya rantsar a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta a Fadar Shugaban Kasa da ke birnin tarayya Abuja.

Shugaba Tinubu ya mika sunayen mutane 48 da ya ke son nada wa minista domin majalisar dattawa ta tantance su.

Yadda Keyamo ya zama ministan Tinubu

Amma, majalisar ta tantance mutane 45 ne kawai cikin 48 din, inda ta bada dalilin batun tsaro na dage tantance sauran mutanen uku.

Kara karanta wannan

Jerin Jiga-Jigan PDP Da Shugaban Kasa Bola Tinubu Ya Bai Mukami

Keyamo, a baya ya yi aiki a matsayin karamin ministan kwadago a karkashin gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Yayin da ya ke aiki a matsayin minista, Keyamo ya soki lakabin mukamin karamin minista, mukamin da ya ke rike da shi. Hakan ya janyo cece-kuce tsakanin masu bibiyan harkokin siyasa a Najeriya.

A yayin zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, ministan ya yi aiki a matsayin kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar APC.

Tinubu Ya Dakatar Da Wasu Ayyuka 2 Da Buhari Ya Fara

Shugaba Tinubu, ta hannun Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya bada umurnin dakatar da sallama filin tashin jiragen sama da kamfanin jirgin sama na kasa.

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, sallama filin tashin jiragen saman da jirgin sama na kasa na cikin manyan ayyukan da tsohuwar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi a bangaren sufurin jiragen sama.

Kara karanta wannan

Dalilin Da Yasa Na Yi Mamaki Da Tinubu Ya Nada Ni Ministan Abuja, Wike

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164