An Dakatar Da Shugaban Karamar Hukumar Da Ya Zargi Gwamna Abiodun Da Karkatar Da Kudade

An Dakatar Da Shugaban Karamar Hukumar Da Ya Zargi Gwamna Abiodun Da Karkatar Da Kudade

  • An yi wani ɗan ƙwarya-ƙwaryar rikici a ƙaramar hukumar Ijebu ta Gabas wajen shugabanta Wale Adedayo
  • An bayyana cewa Adedayo ya zargi gwamna mai ci na jihar Ogun, Dapo Abiodun da baɗaƙalar kuɗaɗe
  • Hakan ne ya janyo ma sa fushin gwamnan, wanda ya kai ga kansilolinsa sun dakatar da shi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Ogun - Rikici ya kunno kai a jihar Ogun, yayin da kansiloli suka dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Ijebu ta Gabas, wanda ya zargi gwamnan jihar Dapo Abiodun da baɗaƙalar kuɗaɗe.

Da safiyar Alhamis ne jami'an tsaro ɗauke da makamai tare da wasu 'yan daba sun kutsa kai sakatariyar ƙaramar hukumar da ke Ogbere duk a cikin yunƙurin tsige shugaban kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

An dakatar da shugaban ƙaramar hukuma bisa zargin gwamna
An dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Ijebu ta Gabas bisa zargin gwamna Abiodun da wawurar kuɗaɗe. Hoto: Dapo Abiodun
Asali: Twitter

Zargin da shugaban ƙaramar hukumar ya yi wa gwamna

Kara karanta wannan

Dirama Yayin Da Shugabannin Kananan Hukumomi Suka Duka a Gaban Gwamna Kan Abu 1, Bidiyon Ya Bayyana

Dakataccen shugaban ƙaramar hukumar wato Wale Adedayo, ya rubuta wasiƙa ne zuwa ga tsohon gwamnan jihar Segun Osoba da kuma hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC).

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cikin wasiƙar ta sa ya zargin Gwamna Abiodun da karkatar da kuɗaɗen ƙananan hukumomin jihar zuwa wani wurin domin biyan buƙatun kansa kamar yadda The Punch ta wallafa.

Wannan zargin ne ake kyautata zaton ya janyowa shugaban ƙaramar hukumar dakatarwa daga kansilolinsa waɗanda bisa ga dukkan alamu suna goyon bayan Gwamna Abiodun.

Sun dakatar da Wale Adedayo ne har na tsawon watanni uku bisa wasu tuhume-tuhume da suka bijiro ma sa da su.

Gwamna Abiodun ya musanta zargin karkatar da kuɗaɗe

A nasa ɓangare, Gwamna Dapo Abiodun ya musanta zargin da Wale Adedayo ya yi ma sa, inda ya bayyana cewa gwamnatinsa na ƙoƙarin bai wa ƙananan hukumomi haƙƙoƙinsu domin ba su damar yin aikace-aikace.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu Zata Ɗauki Sabbin Ma'aikata 300,000 a Faɗin Najeriya, Sahihan Bayanai Sun Fito

A cikin wani ɗan gajeren bidiyo da ya yaɗu a Intanet, an ga shugabannin ƙananan hukumomin jihar sun duƙa suna bai wa gwamnan haƙuri bisa zargin da aka yi ma sa.

Shugaban ƙaramar hukumar da aka dakatar ya yi martani da cewa ya yi rantsuwar cewa zai yi aiki bisa gaskiya don ci gaban ƙasa, saboda haka ba ya tsoron duk abinda zai same shi.

An bayyana cewa jami'an hukumar tsaro na farin kaya (DSS), sun gayyace shi dangane da zargin da ya yi wa gwamnan.

Ma'aikatan ƙananan hukumomi sun shiga yankin aiki a Filato

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan yajin aikin sai baba ta gani da ɗaukacin ma'aikatan ƙananan hukumomin jihar suka shiga.

Hakan ya samo asali daga mayar da dakatattun shugabannin ƙananan hukumomin jihar da aka yi kan muƙamansu, wanda ake ganin hakan ka iya janyo rikici.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng