Karamar hukuma a Yobe ta saka fitilun kan hanya 44 don yin maganin masu kai hari

Karamar hukuma a Yobe ta saka fitilun kan hanya 44 don yin maganin masu kai hari

An saka fitilun kan hanya masu amfani da hasken rana guda 44 a garin Kanamma, hedikwatar karamar hukumar Yunusari a jihar Yobe, domin magance yawaitar kai hare-haren 'yan Boko Haram garin.

An saka fitilun a kan iyakar garin da jamhuriyar Nijar da sansanin sojoji da wurin yanka dabbobi da filin masallacin idi.

Da yake kaddamar da aikin a ranar Talata, mukaddashin shugaban karamar hukumar Yunusari, Musa K Doguna, ya ce aikin na hadin gwuiwa ne da wata kungiya 'Northeast Regional Initiave (NERI)' domin inganta tsaro a garin.

Ya ce saka fitilun zai bawa mutanen garin da jami'an tsaro damar ganin motsin mutane da daddare, wanda hakan zai basu damar ganin masu kawo hari da daddare.

Karamar hukuma a Yobe ta saka fitilun kan hanya 44 don yin maganin masu kai hari
Karamar hukuma a Yobe ta saka fitilun kan hanya 44 don yin maganin masu kai hari
Asali: Twitter

A cewar sa: "fitilun kan hanyar zasu taimaka matuka wajen dakile yawan hare-haren da ake kai wa a kan jama'ar garin da daddare."

DUBA WANNAN: Mun kashe kaifin kungiyar Boko Haram - Gwamnatin Najeriya

Ya kara da bayyana cewar karamar hukumar tare da hadin gwuiwa da NERI, ta gina sakatariyar karamar hukuma, kananan asibitoci, da taimakon manoma da matasa da mata marasa karfi..

Ya yiwa NERI godiya bisa tallafa wa rayuwar jama'ar yankin, tare da kara yin rokon wasu aiyuka a kauyukan kewayen Yunusari.

Shugaban NERI. Abatcha Kachalla, ya ce saka fitilun kan hanyar na daga cikin matakai da dama da suka dauka domin kare rayuwa da dukiyar jama'ar yankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng