Tsare-tsaren Tinubu Za Su Amfani 'Yan Najeriya a Gaba Idan Aka Yi Hakuri, Gwamna Sanwo-Olu Na Legas

Tsare-tsaren Tinubu Za Su Amfani 'Yan Najeriya a Gaba Idan Aka Yi Hakuri, Gwamna Sanwo-Olu Na Legas

  • Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya buƙaci 'yan Najeriya su ƙara haƙuri da tsare-tsaren Tinubu
  • Ya ce abubuwa ne masu muhimmanci shugaban ya zo da su, wanda nan gaba kadan 'yan ƙasa za su dara
  • Sanwo-Olu ya kuma jinjinawa mai ɗakin shugaban ƙasa kan tsare-tsaren tallafin mata da ta zo da su

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya buƙaci 'yan Najeriya su ƙara haƙuri da juriya kan sabbin tsare-tsaren da aka zo da su a gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 30 ga watan Agusta a yayin da ya ziyarci matar shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu kamar yadda jaridar Leadership ta wallafa.

Gwamnan jihar Legas ya bukaci 'yan Najeriya su ƙara haƙuri da tsare-tsaren Tinubu
Gwamnan Legas ya ce za a ji dadin tsare-tsaren Shugaba Tinubu a nan gaba. Hoto: Sen. Oluremi Tinubu, CON
Asali: Facebook

Tsare-tsaren Tinubu za su amfani 'yan Najeriya a gaba

Kara karanta wannan

Babban Malamin Addini Ya Fadi Wadanda Ya Kamata Tinubu Ya Bincika Don Ciyar Da Najeriya Gaba

Sanwo-Olu ya bayyana cewa Shugaba Tinubu na iya bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya gyara ƙasar nan ta yadda kowane ɗan Najeriya zai ji daɗin rayuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A dalilin hakan ne ya ce ya zama wajibi shugaban ya ɗauki tsauraran matakan da ya ɗauka a yanzu, wanda suke buƙatar juriya da haƙurin 'yan Najeriya domin a cimma nasara.

Ya ƙara da cewa dole ne jama'a su sha wahala a halin da ake ciki, amma daga bisani kowa zai samu ingantacciyar rayuwa, kuma tattalin arziƙin ƙasa zai bunƙasa.

Sanwo-Olu ya jinjinawa Oluremi Remi Tinubu

A ci gaba da jawabinsa, Gwamna Sanwo-Olu ya kuma jinjinawa mai ɗakin shugaban ƙasa Oluremi Tinubu, kan tsarukan taimakawa mata da ta zo da su.

Ya ce tsarin da Remi Tinubu ta zo da shi na ‘Renewed Hope Initiative, zai taimaka matuƙa, wajen samun nasara a tsarin ‘Renewed Hope Agenda’ da Shugaba Tinubu ya zo da shi.

Kara karanta wannan

Hantar Tinubu Ta Kaɗa, Shugaban Jam'iyya Ya Faɗi Wanda Yake da Tabbacin Zai Samu Nasara a Kotu

Ya kuma jinjinawa Remo Tinubu kan yadda tsarin na ta ya karkata a ɓangaren makarantu da kuma ɓangaren tallafawa mabuƙata kamar yadda TVC News ta wallafa.

Minista ya fadi dalilin da ya sa Tinubu ya cire tallafin man fetur

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan jawabin da ministan yaɗa labarai, Mohammed Malagi ya yi kan dalilin Shugaba Tinubu na cire tallafin man fetur.

Ya ce 'yan Najeriya za su ya baƙar wahala a yanzu, amma kuma za su ji dadi sosai a gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng

Online view pixel