Kamata Ya Yi Tinubu Ya Binciki Wasu Daga Cikin Manyan Ma'aikatun Gwamnati, In Ji Primate Ayodele

Kamata Ya Yi Tinubu Ya Binciki Wasu Daga Cikin Manyan Ma'aikatun Gwamnati, In Ji Primate Ayodele

  • Shugaban ‘INRI Evangelical Spiritual Church’, Primate Ayodele, ya ce sai an riƙa bincikar masu riƙe da mukamai za a samu sauyi
  • Ayodele ya ce dole ne Tinubu ya binciki babban kamfanin mai NNPCL, babban bankin Najeriya da hukumar kwastam
  • Ya ce akwai bukatar bincikar waɗannan bangarori domin hana yaɗuwa cin hanci zuwa wasu ɓangarorin daban

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Shugaban ‘INRI Evangelical Spiritual Church’, Primate Elijah Ayodele, ya buƙaci Tinubu ya gudanar da bincike a wasu ma'aikatun gwamnati.

Elijah ya bayyana hakan ne a cikin wani ɗan guntun bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X a cikin 'yan kwanakin nan.

An shawarci Tinubu kan abinda zai yi don ciyar da Najeriya gaba.
Primate Elijah Ayodele ya shawarci Tinubu kan abinda ya kamata ya yi domin ciyar da Najeriya gaba. Hoto: Primate Babatunde Elijah Ayodele, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Elijah ya ce Najeriya ba za ta ci gaba ba sai Tinubu ya yi bincike

Primate Elijah ya ce muddun Shugaba Bola Tinubu bai saurari shawarar da ya ba shi ba, to dole cin hanci zai ci gaba da yaɗuwa a ma'aikatu daban-daban.

Kara karanta wannan

Hadimin Atiku Ya Fadi Iya Wa'adin Da Ya Ragewa Bola Tinubu a Kan Kujerar Shugabanci, Ya Ba Shi Shawara

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya kuma ce rashin gudanar da binciken a kan wasu ma'aikatun gwamnati zai iya kawowa Najeriya da kuma gwamnatin ta Tinubu cikas.

Ya ƙara da cewa muddun ana so Najeriya ta ci gaba, to dole ne a gudanar da bincike a kan kamfanin mai na Najeriya (NNPCL), babban bankin Najeriya (CBN), hukumar kwastam da sauransu.

Elijah ya aika saƙon gargadi ga 'yan majalisun Najeriya

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa a baya, kun karanta saƙon gargaɗin da Primate Elijah Ayodele ya aikewa 'yan majalisun Najeriya kan yadda suke tafiyar da al'amuransu.

Ya shawarcesu 'yan majalisun da su riƙe addu'a su kuma yi abinda ya dace a mazaɓunsu saboda ya hango cewa ana yi wa wasu daga cikinsu ruwan duwatsu.

Atiku ya gano tsaikon da zai kwace kujerar Tinubu da shi

Kara karanta wannan

PSC: Shugaba Tinubu Ya Sallami Manyan Jami'ai DIG 4, Ya Naɗa Waɗanda Zasu Maye Gurbinsu

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan shari'ar bayan zaɓe da ake ci gaba da yi tsakanin Atiku da Bola Ahmed Tinubu.

A cikin 'yan kwanakin nan ne Atiku ya yi zargin cewa babu bayanan makarantun Firamare da na Sakandare a cikin bayanan karatun Shugaba Tinubu.

Ya ce hakan ya ci karo da bayanan da Tinubu ba da a lokacin da ya nemi kujerar gwamnan Legas a shekarar 1999.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng