Kashim Shettima Ya Ce Najeriya Na Cikin Gagarumar Matsala Ta Fuskar Tattalin Arziƙi

Kashim Shettima Ya Ce Najeriya Na Cikin Gagarumar Matsala Ta Fuskar Tattalin Arziƙi

  • Kashim Shettima, ya shaidawa kwamitin garambawul ga harkokin tattara kuɗaɗe da su gaggauta yin abinda ya dace
  • Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi baƙuncin shugaban kwamitin Taiwo Oyedele a ofishinsa ranar Litinin
  • Shettima ya bukaci kwamitin ya yi aiki tuƙuru wajen farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasa cikin gaggawa

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya buƙaci kwamitin yin garambawul kan harkokin tattara kuɗaɗen shiga da su yi gaggawar yin abinda ya dace domin farfaɗo da tattalin arziƙin Najeriya.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ( wanda ake kira Twitter a da), Kashim ya bayyana cewa ya karɓi baƙuncin 'yan kwamitin ƙarƙashin jagorancin Taiwo Oyedele.

Kashim Shettima ya ce Najeriya na cikin gagarumar matsala
Kashim Shettima ya ce Najeriya na cikin babbar matsala kan samun kuɗaɗen shiga. Hoto: @officialSKSM
Asali: Twitter

Kashim Shettima ya buƙaci kwamitin ya ƙara ƙaimi

Kara karanta wannan

An Bayyana Wanda Ya Fi Dacewa Ya Zama Ministan Matasa a Gwamnatin Shugaba Tinubu

Shettima ya buƙaci kwamitin da ya yi aiki cikin gaggawa wajen gyara tattalin arziƙin Najeriya ta hanyar magance matsalolin da ake fuskanta wajen tattara kuɗaɗe, wanda shi ne ƙashin bayan arziƙin kowace ƙasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana cewa Najeriya na cikin gagarumar matsala a halin da ake ciki, amma ya nuna kwarin gwiwarsa kan kwamitin inda ya yi fatan za su yi abinda ya dace.

Shettima ya ƙara da cewa rashin ingantaccen shugabanci ya dabaibaye Najeriya, amma yana da yaƙinin cewa Shugaba Bola Tinubu zai yi ƙoƙarin daidaita al'amura ya kuma kawo ma ta ci gaba.

Hadimin Atiku ya shawarci Tinubu ya naɗa Fani-Kayode minista

A baya Legit.ng ta yi rahoto kan shawarar da hadimin Atiku Abubakar wato Daniel Bwala ya bai wa shugaban ƙasa Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu Ta Bayyana a Yanayin Da Ta Tarar Da Tattalin Arziƙin Najeriya

Ya ce kamata ya yi Tinubu ya naɗa Femi Fani-Kayode a matsayin minista a gwamnatinsa duba da irin gudummawar da ya ba shi a lokacin yaƙin neman zaɓe.

Bwala ya ce hakan shi ne abinda ya kamata Tinubu ya yi kafin Atiku ya karɓe kujerarsa nan da watanni biyu masu zuwa.

Shettima ya bayyana yadda cire tallafi zai kare lafiyar al'umma

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan yadda cire tallafin man fetur da Tinubu ya yi zai amfani 'yan Najeriya ta ɓangaren kiwon lafiya.

Ya ce cire tallafin zai taimaka wajen kare 'yan Najeriya daga shaƙar gurɓatacciyar iska mai tarin yawa, wacce ta ke shafar lafiyar ɗan adam.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng