Hannatu Musawa: Shin Masu Yi Wa Kasa Hidima Na Iya Zama Minista? Falana, Sauran Lauyoyi Sunyi Martani

Hannatu Musawa: Shin Masu Yi Wa Kasa Hidima Na Iya Zama Minista? Falana, Sauran Lauyoyi Sunyi Martani

  • Masana shari'a a Najeriya sun yi sabani akan cancantar nada Hannatu Musawa, wata mai bautar kasa (NYSC), a matsayin minista da Shugaba Bola Tinubu yayi
  • Wasu daga cikin lauyoyin na ganin hakan ya dace kundin tsarin mulki kuma bai saba da dokar NYSC ba, yayin da wasu, ciki har da Falana basu amince ba
  • Cece-kucen ya fara ne bayan Hukumar NYSC ta tabbatar da Musawa a matsayin yar bautar kasa

FCT, Abuja - Manyan lauyoyi a Najeriya na cigaba da tafka muhawara kan sahihancin nada Hannatu Musawa, wadda bata kammala bautar kasa ba, a matsayin ministar bunkasa al'adu da shugaba Tinubu yayi.

Yayin da wasu lauyoyin ke cewa hakan bai sabawa doka ba, wasu basu amince ba.

Shin wanda ke NYSC na iya zama minista a Najeriya
Masana shari'a sun bada mabanbantan ra'ayoyi dangane da halarcin nadin Musa Hannatu matsayin minista yayin da ta ke hidimar kasa. Hoto: credit: @madiba_ledum
Asali: Twitter

Musawa na daga cikin ministoci 45 da sanatoci suka tantance kuma shugaba Tinubu ya rantsar.

Kara karanta wannan

NYSC: Hannatu Musawa Ta Sake Sabon Martani Game Da Bautar Kasa, Ta Gargadi Mutane

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai dai, bayan wani zargi da wata kungiya HURIWA ta yi, hukumar NYSC ta tabbatar har yanzu yar bautar kasa ce, ta kuma kara da cewa karbar irin wannan mukami ya saba da dokar NYSC.

Hannatu Musawa: Ra'ayin Lauyoyi

Da ya ke sharhi akan batun, Norrison Quakers (SAN) ya yabawa Shugaba Tinubu, yana mai cewa hakan tallafawa matasa ne, kamar yadda ThisDay ta ruwaito.

"Na kalli dokar, kuma banga inda hakan ya zama laifi ba. Na kuma duba sashe na biyu na dokar NYSC, ba wata doka da ta ce, dole sai ta kammala bautar kasa kafin a iya nada ta minista a Najeriya," kamar yadda ya bayyana.

Da yake nasa sharhin, Dakta Abiodun Layonu (SAN) ya ce tunda abin da abin da doka ke da bukata kafin zama dan majalisar wakilan tarayya ita ce shaidar kammala makaranta, shima zama minista haka ya kamata ya zama.

Kara karanta wannan

Ba Za Ta Yi Wu Ba: Tinubu Ya Bayyana Tsari 1 Na Buhari Da Ba Zai Cigaba Da Shi Ba

Tsohon sakataren kungiyar manyan lauyoyi ta Najeriya, Seyi Sowemimo (SAN), shima ya ce kasancewar ta yar bautar kasa ba zai hana Hannatu Musawa zama minista ba.

Falana ya soki nada Musawa

Sai dai, lauyan kare hakkin dan Adam, Femi Falana (SAN), ya soki nadin Musawa. A cewarsa, mai bautar kasa ba shi da cancantar zama minista.

Falana na ganin cewa duk wanda bai yi bautar kasa ba bai kamata yayi wakilci a majalisar tarayya ba, ya kara da cewa kundin tsarin mulki ya shimfida irin wannan ka'idojin don zama minista.

Shima, Dayo Akinlaja (SAN) ya ce nada Musawa ya sabawa dokar NYSC.

Ya yi bayanin cewa dokar ta ce dole kowane mai bautar kasa yayi aikin watanni 12 a jere.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164