Kotun Daukaka Kara Ta Tsige Shugaban LP, Ta Tabbatar da Apapa

Kotun Daukaka Kara Ta Tsige Shugaban LP, Ta Tabbatar da Apapa

  • Tsagin jam'iyyar LP karkashin Lamidi Apapa ya yi nasara kan tsagin Abure a Kotun ɗaukaƙa ƙara mai zama a Owerri, jihar Imo
  • A ranar Alhamis, 24 ga watan Agusta, 2023, Kotun ta tsige Abure kuma ta tabbatar da Apapa a matsayin shugabam LP ta ƙasa
  • Ta kuma umarci INEC ta amince tare da buga sunayen yan takarar gwamna a jihohi 3 da tsagin Apapa ya gabatar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Owerri, Jihar Imo - Kotun daukaka kara mai zama a Owerri, babban birnin jihar jihar Imo ta tsige Julius Abure, daga kujerar shugaban jam'iyyar Labour Party (LP) na ƙasa.

Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa bayan tunɓuke Mista Abure, Kotun ta kuma amince da Lamidi Apapa a matsayin halastacccen shugaban jam’iyyar LP ta kasa.

Rikicin shugabanci a Labour Party.
Kotun Daukaka Kara Ta Tsige Shugaban LP, Ta Tabbatar da Apapa Hoto: Julius Abure
Asali: Facebook

Haka zalika Kotun ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta karɓa tare da buga sunayen duk ‘yan takarar gwamna da kwamitin ayyuka na kasa karkashin jagorancin Apapa ya gabatar a jihohin Imo, Bayelsa, da Kogi.

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: SSG Mace Ta Ayyana Burinta Na Shiga Takarar Gwamna a Jihar APC a Zaɓen 2024

Kotun ta kuma yi watsi da takarar Sanata Athan Achonu a matsayin ɗan takarar gwamna a jihar Imo, da wasu na 'yan takara na bangaren LP da Abure ke jagoranta, PM News ta tattaro.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yadda rikicin shugabanci ya addabi Labour Party

A watan Afrilu, Apapa ya ce dakatarwar da aka yi masa daga matsayin mamban jam’iyyar ba daidai bane, inda ya jaddada cewa shi ne halastaccen shugaban riko na LP.

A ranar 14 ga watan Agusta, Kotun ɗaukaka kara mai zama a Benin, babban birnin jihar Edo, ta tabbatar da Abure a matsayin shugaban LP na halal.

Sakataren watsa labarai na jam'iyyar LP ta ƙasa, Obiora Ifoh, shi ne ya bayyana hukuncin da Kotun ta yanke a wata sanarwa da ya fitar.

Gabanin wannan lokaci, babbar kotun jihar Edo ta yi fatali da dakatarwan da wasu mambobin LP suka yi wa Abure a matakin gunduma.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin Da Jami'ar Chicago Ta Amince Ta Saki Takardun Karatun Shugaba Tinubu, Akwai Sharadi

Mai shari'a Emmanuel Aihamoje na babbar Kotun jiha mai zama Edo ne ya yi fatali da ƙarar bisa rashin cancanta, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Ondo 2024: SSG Ta Ayyana Shirinta Na Tsaya Wa Takarar Gwamna

A wani rahoton kuma kun ji cewa, Sakatariyar gwamnan jihar Ondo ta ayyana burinta na neman takarar gwamna a zaben 2024.

SSG ta bayyana cewa jihar Ondo na buƙatar mace a matsayin gwamna kuma a shirye take ta gaji gwamna Akeredolu na APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262