Jami'an Yan Sanda Sun Mamaye Babbar Sakatariyar APC Da Ke Abuja
- Jami'an rundunar yan sanda sun mamaye sakatariyar APC ta ƙasa da ke birnin Abuja ranar Alhamis, 24 ga watan Agusta, 2023
- Rahotanni sun nuna cewa hakan na zuwa ne yayin da APC ke shirin rantsar da sabbin mambobin kwamitin NWC na ƙasa
- Tuni gwamna Yahaya Bello ya dira wurin bayan jam'iyyar ta yi fatali da ɗan takarar da ya aiko mata daga Kogi
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT Abuja - Dakarun 'yan sanda cikin shirin ko ta kwana sun kewaye babbar sakatariyar jam'iyyar APC ta ƙasa da ke birnin tarayya Abuja ranar Alhamis 24 ga watan Agusta.
Jaridar Vangaurd ta tattaro cewa 'yan sandan sun yi wa Sakayariyar tsinke ne yayin da jam'iyyar APC ke shirin rantsar da sabbin mambobin kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC).
Rahoton ya nuna cewa dakarun 'yan sanda mara adadi sun mamaye 'Blantyre Street Entrance, wurin da hedkwatar jam'iyyar APC take a Abuja.
Meyasa yan sanda suka ɗauki wannan matakin?
Har ila yau, ɗaruruwan mutanen da suka ɓalle da zanga-zanga a hedkwatar APC sun nuna ko ajikinsu da yadda aka ƙara girke dakarun 'yan sanda.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An ce gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya isa Sakateriyar APC da wuri-wuri yau Alhamis kuma ana ganin hakan ya ƙara haddasa tashin hankali a yankin.
APC ta wayi gari cikin rigingimu ne biyo bayan sanar da Mary Alile Idele daga jihar Edo, shiyyar Kudu maso Kudu a matsayin sabuwar shugaban mata ta ƙasa.
Bayanai sun nuna ita ce zaɓin Sanata Adams Oshiomhole yayin da aka yi fatali da Stella Odey-Ekpo, wacce Betta Edu, ministar jin ƙai ke goyon baya.
Rigima ta kaure a APC kan sabbin mambobin NWC
Haka zalika APC ta sanar da naɗa Duro Meseko (Jihar Kogi) a matsayin sabon mataimakin sakataren watsa labarai na ƙasa (Arewa ta Tsakiya) wanda zai maye gurbin Yakubu Ajaka.
An tattaro cewa James Faleke ne ya bai wa APC shawarin naɗa Meseko maimakon ɗan takarar da gwamna Yahaya Bello yake so, Channels tv ta rahoto.
Edu, tsohuwar shugabar mata ta dira Sakatariyar APC da misalin ƙarfe 6:20 na daren jiya Laraba domin nuna rashin jin daɗinta kan sauya sunan wacce ta turo, ta bar wurin mintuna 45 bayan haka.
A nasa ɓangaren, gwamna Bello na Kogi ya dira sakatariyar kuma ya shaida wa 'yan jarida cewa ba zai je ko ina ba har sai an shawo kan lamarin. Ya ce, "Dole a warware batun yau."
Gwamnatin Abba Gida-Gida Ta Gano Makaranta Mai Dalibai 5,000 Da Babu Azuzuwa
A wani rahoton na daban Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta bankaɗo wasu matsaloli da suka dabaibaye ɓangaren ilimi a jihar Kano.
Kwamishinan ilimi na jihar Kano , Umar Haruna Doguwa, shi ne ya bayyana haka ranar Laraba yayin da ya karɓi bakuncin wakilan Burtaniya a ofishinsa.
"Akwai Babbar Matsala" Fitaccen Malami Ya Bayyana Hukuncin da Kotu Zata Yanke Kan Nasarar Tinubu a 2023
Asali: Legit.ng