Atiku/Obi Vs Tinubu: Malami Ya Bayyana Hukuncin da Kotu Zata Yanke Kan Zaben 2023

Atiku/Obi Vs Tinubu: Malami Ya Bayyana Hukuncin da Kotu Zata Yanke Kan Zaben 2023

  • Malamin coci, Fasto Tony Anthony, daga Bode a jihar Abiya ya bayyana wahayin da aka masa kan karar da ke gaban Kotun zaɓe
  • Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar LP, Peter Obi, ya shigar ƙara gaban Kotun yana kalubalantar sakamakon zaben 25 ga watan Fabrairu
  • Haka zalika takwaransa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya tunkari kotun sauraron ƙararrakin zaben shugaban ƙasa, ya kalubalanci nasarar APC

FCT Abuja - Fitaccen Malami kuma shugaban majami'ar 'Spiritual head of the Souls For Christ Ministry', Apostle Tony Anthony, ya yi hasashen hukuncin da Kotun sauraron kararakin zabe zata yanke.

Faston ya bayyana cewa kotun PEPC zata ƙara tabbatar da nasarar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Shugaba Tinubu, Atiku da Kwankwaso.
Atiku/Obi Vs Tinubu: Malami Ya Bayyana Hukuncin da Kotu Zata Yanke Kan Zaben 2023 Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar, Mr Peter Obi
Asali: Facebook

A wani wahayi da ya ce an masa a shafinsa na Facebook, Malamin cocin ya ce duk da hukuncin da Kotu zata yanke, "Na hango wani karfi ya kawar da Tinubu daga mulki."

Kara karanta wannan

Babban Malamin Addini Ya Hango Wani Sabon Abu Da Zai Faru a Mulkin Shugaba Tinubu

Wane hukunci Kotun zaɓe zata yanke kan zaɓen 2023?

Bayan tabbatar da cewa Tinubu ne zai ƙara samun nasara a Kotu, Malamin ya bayyana wasu wahayoyin da aka masa marasa daɗi game da Najeriya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya rubuta cewa:

"Wahayi: Na hango tashin hankali a Najeriya, na ga iyaye suna hana 'ya'yansu zuwa makaranta, na ga ma'aikatan gwamnati da masu zaman kansu sun daina zuwa aiki."
"Na hango kotun sauraron korafe-ƙorafen zaben shugaban ƙasa ta tabbatar da nasarar Bola Tinubu. Na hango wani ƙarfin cin mutunci ya kori Tinubu daga kan mulki."
“Na ga Najeriya a cikin wani hali na tsananin bakin ciki. Na ga kujerar shugaban kasa babu kowa, sai na ga maza masu kaya iri-iri da kalar tufafi daban-daban suna kokawa a kanta."

Faston ya ci gaba da cewa:

Kara karanta wannan

"Akwai Haske": Abdulsalami Ya Yi Magana Kan Tattaunawarsu Da Sojojin Juyin Mulkin Nijar

“Na ga kasashen waje sun kawo ɗauki a Najeriya. Na ga Tinubu ya gudu ya ɓuya. Na ga guguwar ruwa tana ruri a kan Najeriya. Duk waɗannan za su faru da sauri tsakanin 3 zuwa 7 kamar yadda na ga an rubuta."
"Yana nufin sau 3 a cikin kwanaki 7 ma'ana a cikin kwanaki 21 haka zata faru kamar yadda aka fassara mun. Ubangiji ya yi matukar fushi da shugabannin Najeriya.”

Jam'iyyar PDP Ta Dakatar da Shugaban Matasa

A wani rahoton kuma Kwamitin gudanarwa na PDP reshen jihar Kwara ya dakatar da shugaban matasan jam'iyya, Prince Haliru Dansoho Mahmoud.

Wannan matakin ya biyo bayan karɓan rahoton kwamitin ladabtarwa da aka kafa bayan mambobin PDP sun kai ƙorafi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262