Jam'iyyar PDP Ta Dakatar da Shugaban Matasa Na Jihar Kwara Sai Baba Ta Gani
- Kwamitin gudanarwa na PDP reshen jihar Kwara ya dakatar da shugaban matasan jam'iyya, Prince Haliru Dansoho Mahmoud
- Wannan matakin ya biyo bayan karɓan rahoton kwamitin ladabtarwa da aka kafa bayan mambobin PDP sun kai ƙorafi
- Tun a baya, shugaban matasan ya jagoranci mambobi inda suka nemi shugabanni su yi bayanin yadda aka kashe kuɗin zabe a Kwara
Kwara State - Jam’iyyar PDP reshen jihar Kwara ta dakatad da shugaban matasa, Mista Dansoho Mahmoud, har sai baba ta gani, bisa zargin tafka kura-kurai a harkokin tafiyar da jam'iyyar.
Punch ta rahoto cewa PDP ta tabbatar da ɗaukar wanna matakin ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun sakataren watsa labarai na jiha, Prince Tunji Morohunfoye.
Ya ce kwamitin gudanarwa na jihar Kwara (SWC) ya amince da dakatar da shugaban matasan PDP, Mahmoud, a taron da ya gudana ranar Talata, 22 ga watan Agusta.
A rahoton Daily Trust, wani sashin sanarwan ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Jam’iyyar PDP reshen jihar Kwara ta cimma matsaya bayan taron kwamitin gudanarwa na jiha wanda ya gudana ranar Talata, 22 ga watan Agusta, 2023."
"Taron ya biyo bayan samun rahoton kwamitin ladabtarwa da jam'iyyar ta kafa musamman domin bincikar batun rashin ɗa'a da kura-kuran da ake zargin shugaban matasa, Prince Haliru Dansoho Mahmoud, ya aikata."
"Rahoton kwamitin ya nuna cewa shugaban matasan PDP na Kwara ya aikata zargin da mambobi ke masa. Bisa haka SWC ya yanke dakatar da shi har sai baba ta gani."
Wane kuskure shugaban matasan ya aikata?
Tun asali dai shugaban matasan PDP na Kwara, Mahmoud, ya jagorancin gungun mambobi sun kalubalanci yadda shugabannin jam'iyya suka kashe kuɗin babban zaɓen 2023.
Ya ce:
"Bana buƙatar a titsiye kowa, kawai ina son SWC ya fito ya mana bayanin yadda kuɗin da uwar jam'iyyar ta ƙasa ta turo jihar Kwara domin tunkarar babban zaɓe 2023 suka ɓata."
Rikicin PDP: Makinde Da Sauran Yan G5 Sun Yi Gum Yayin da Wike Ya Kama Aikin Minista a Gwamnatin APC
Bayan haka ne, jam'iyyar PDP ta kafa kwamitin ladabtarwa a watan Yuni domin duba waɗannan ƙorafe-korafen.
Gwamna Aliyu Ya Raba Wa Sabbin Kwamishinoni Muƙamai
A wani rahoton na daban Gwamna Ahmad Aliyu na jihar Sakkwato ya raba muƙamai ga sabbin kwamishinoni da ya rantsar ranar Talata.
Legit.ng Hausa ta tattaro muku jerin sunayen kwamishinoni 25 da suka karbi rantsuwar kama aiki a jihar Sakkwato da kuma ma'aikatun da aka tura su.
Asali: Legit.ng