Uwargidan Shugaba Tinubu Ta Ce 'Yan Najeriya Za Su Ji Dadi Nan Gaba Kadan

Uwargidan Shugaba Tinubu Ta Ce 'Yan Najeriya Za Su Ji Dadi Nan Gaba Kadan

  • Uwargidan shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu ta bai wa 'yan Najeriya haƙuri kan halin da ake ciki
  • Ta roƙi 'yan Najeriya sun hango ci gaban da tsare-tsaren Tinubu za su kawowa ƙasar a gaba
  • Ta bayyana cewa mijin na ta na nufin 'yan Najeriya da alkhairi, kuma yana bakin ƙoƙarinsa wajen ganin sun samu sauƙi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta tabbatarwa da 'yan Najeriya cewa mai gidanta na nufin 'yan Najeriya da alkhairi duk da halin ƙuncin da ake ciki.

Ta nemi 'yan Najeriya su hango amfanin da hakan zai haifar a gaba na fatan samun ci gaba ga ƙasar baki ɗaya.

Ta bayyana hakan ne a yayin da ta karɓi baƙuncin matan shugabannin hukumomin tsaron Najeriya kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa.

Kara karanta wannan

Aljeriya Na Ba Nijar Wutar Lantarki Kyauta Bayan Najeriya Ta Dai Na Ba Su? Gaskiya Ta Bayyana

Remi Tinubu ta bai wa 'yan Najeriya haƙuri kan halin da ake ciki
Uwargidan Shugaba Tinubu ta ce 'yan Najeriya za su ji daɗi a gaba. Hoto: Sen. Oluremi Tinubu
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

'Yan Najeriya za su ji dadin tsare-tsaren a gaba

Oluremi Tinubu ta bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu na yin iya bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya ragewa 'yan ƙasa raɗaɗin da cire tallafin man fetur ya jefa su ciki.

Ta jaddada cewa za a ji dadi a gaba da zarar tsare-tsaren da Tinubu ya zo da su sun fara aiki yadda ya kamata.

Ta ƙara da cewa ƙara da cewa shirinta na ‘Renewed Hope Initiative’ zai taimakawa ƙudurorin gwamnati, wanda a dalilin hakan ne ma take neman haɗin kan matan shugabannin tsaron.

Shugaba Tinubu ya shiga wata ganawa da manyan ECOWAS

A wani labarin na daban da Legit.ng ta kawo a baya, kun karanta cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya shiga wata ganawa ta sirri da wasu daga cikin manyan ECOWAS a fadar Gwamnatin Tarayya.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: An Bankado Wani Sabon Tuggu Da Tinubu Ke Shiryawa a Kan Atiku Abubakar

Hakan dai ba zai rasa nasaba da batun yaƙin da ke shirin ɓarkewa tsakanin ƙungiyar ta ECOWAS da Tinubu ke jagoranta da sojojin juyin mulkin jamhuriyar Nijar ba.

Daga cikin mahalarta taron akwai Nuhu Ribadu, Abdulsalami Abubakar da kuma da kuma Dakta Omar Touray kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta wallafa.

Tinubu zai tsamo 'yan Najeriya miliyan 136 daga talauci

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan batun shirin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke yi na ganin ta tsamo 'yan Najeriya miliyan 136 daga talauci.

Sabuwar ministar jin ƙai da yaye talauci ta ƙasa Dakta Betta Edu ce ta bayyana hakan ranar Litinin, jim kaɗan bayan shigarta ofis domin kama aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng