Shugaba Tunubu Ya Tilastawa Shugaban NIMC Tafiya Hutu, Ya Nada Sabo
- Bola Tinubu ya tilasata wa shugaban hukumar NIMC, Injiniya Aliyu Abubakar Aziz tafiya hutun dole na kwanaki 90
- Shugaban ƙasan ya kuma naɗa muƙaddashin shugaban NIMC da kuma shugaban hukumar DTAC na ƙasa
- Dukkan wannan sauye-sauye na ƙunshe a wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasa ya fitar, ya ce matakan zasu fara aiki nan take
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT Abuja - Shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya umarci shugaban hukumar katin shaidar zaman ɗan ƙasa (NIMC), Aliyu Abubakar Aziz, ya fara hutun ritaya na watanni uku.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa wannan mataki na ƙunshe ne a wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ya fitar ranar Talata, 22 ga watan Agusta, 2023.
Ya ce Datakta Janar/Shugaban hukumar NIMC zai tafi wannan hutu ne daga ranar 24 ga watan Agusta, 2023 wanda zai kai ga lokacin ritayarsa daga aiki ranar 24 ga watan Nuwamba, 2023.
Shugaba Tinubu ya naɗa sabon shugaban NIMC
Sanarwan ta ƙara da cewa:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Shugaban Tinubu ya amince da nadin Injiniya Bisoye Coker-Odusote a matsayin mukaddashin Darakta Janar/Shugaban hukumar NIMC na tsawon kwanaki 90, daga ranar 24 ga Agusta, 2023."
"Bayan wannan lokaci ne sabon shugaban NIMC ɗin zai fara zangon mulkinsa na farko tsawon shekaru huɗu daga ranar 24 ga watan Nuwamba, 2023."
Tinubu ya ƙara yin wani sabon naɗi
Bugu da ƙari, Shugaban ya kuma amince da nadin Honorabul Yusuf Buba Yakub a matsayin sabon shugaban hukumar agajin fasaha (DTAC).
"Wannan naɗi ya biyo bayan karewar wa'adin tsohon shugaban hukumar DTAC, Dakata Pius Osunyikanmi, wanda ya ƙare kwanan nan," inji sanarwan da kakakin shugaban ƙasan ya fitar.
Daƙa karshe, sanarwan ta bayyana cewa waɗannan naɗe-naɗen za su fara aiki ne nan take, kamar yadda NTA News ta wallafa a shafinta na Tuwita.
Jerin Ministocin Shari'a, Antoni Janar da Aka Yi a Najeriya Tun Daga 1999
A wani rahoton na daban kun ji cewa tun bayan dawowar mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999, hazikan ‘yan Najeriya o ne suka riƙe ofishin a lokuta daban-daban.
Mun haɗa muku jerin Ministocin Shari'a da Antoni Janar na Tarayyar tun daga 1999.
Asali: Legit.ng