Shehu Sani Ya Shawarci Wike Ya Bi a Hankali Don Kar Ya Jefa Kansa Da Tinubu Cikin Rigima
- Sabon ministan Birnin Tarayya (FCT) Abuja Nyesom Wike ya shiga ofis domin fara aiki
- Wike mamba ne a babbar jam'iyyar adawa ta PDP da ake yi wa kallon mai son janyo hayaniya
- Dan jam'iyyarsa wato Sanata Shehu Sani ya ba shi shawarar ya bi a hankali don gudun kar a samu matsala
FCT, Abuja - Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya gargaɗi sabon ministan Birnin Tarayya (FCT) Abuja Nyesom Wike.
Ya ce Wike mutum ne jajirtacce a duk aikin da ya tasa a gaba, sai dai ya yi gargaɗin cewa zai iya janyowa kansa da Tinubu matsaloli masu girma.
Nyesom Wike dai na cikin mutane 45 da Shugaba Bola Tinubu ya rantsar a ranar Litinin ɗin da ta gabata domin su kama aiki a matsayin ministoci.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Shehu Sani ya shawarci Wike ya bi a hankali
Sanata Shehu Sani ya shawarci Wike da ya bi a hankali domin gudun kar ya takalo tsuliyar dodo kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X, wanda ake kira da Twitter a baya.
Tsohon sanatan ya aminta da cewa tsohon gwamnan jihar Ribas, wanda yanzu ya zama ministan Babban Birnin Tarayya (FCT) Abuja, ya san aiki sosai yadda ya kamata.
Sai dai ya shawarce shi da ya lura da irin kalamai da ayyukan da yake yi domin gudun kar ya jefa kansa da gwamnatin Shugaba Tinubu cikin rigingimu na siyasa.
Hadimin Atiku ya caccaki Wike kan barazanar rusau
A baya Legit.ng ta kawo rahoto ka martanin da hadimin Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Daniel Bwala ya yi wa ministan Birnin Tarayya Nyesom Wike.
Bwale ya shawarci tsohon gwamnan na Ribas da ya mayar da hankalinsa kan abubuwan da za su amfani al'ummar birnin ba wai barazanar rushe-rushe ba.
Martanin na Bwala ya biyo bayan alwashin da Wike ya yi na rushe duk wani gida da aka gina shi ba bisa ƙa'ida ba a cikin birnin na tarayya.
Tinubu ya yi kira na musamman kan sabbin ministocinsa
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan kira na musamman da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa sababbin ministocinsa a yayin da yake rantsar da su.
Ya nemi sabbin ministocin da su yi aiki tuƙuru inda ya kuma buƙaci su fifita ra'ayi da jin daɗin 'yan Najeriya sama da ra'ayin wani yanki ko wata jiha.
Asali: Legit.ng