An Sha Yar Dirama Yayin da Sabuwar Minista Ta Durkusa a Gaban Tinubu Bayan Rantsarwa, Bidiyon Ya Yadu

An Sha Yar Dirama Yayin da Sabuwar Minista Ta Durkusa a Gaban Tinubu Bayan Rantsarwa, Bidiyon Ya Yadu

  • Daya daga cikin sabbin ministocin Najeriya da aka rantsar ta yi wani abu da ba a taba tunani ba a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta
  • Wani bidiyo da ke nuna lokacin da Lola Ade-John, ministar yawon bude ido ta durkusa a gaban shugaban kasa Bola Tinubu jim kadan bayan karbar rantsuwarta ya bayyana
  • Sabuwar ministar ta haddasa yar dirama bayan ta zabi durkusawa a gaban Tinubu bayan sanya hannu a takardar daukar rantsuwar kama aiki

Abuja - Lola Ade-John, sabuwar ministar yawon bude ido da aka rantsar a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta, ta shiga kanen labarai.

Wasu daga cikin sabbin ministoci yayin rantsarwa
An Sha Yar Dirama Yayin da Sabuwar Minista Ta Durkusa a Gaban Tinubu Bayan Rantsarwa, Bidiyon Ya Yadu Hoto: Federal Ministry of Information and Culture, Nigeria
Asali: Facebook

Hakan ya kasance ne yayin da Ade-John ta je gaishe da shugaban kasar Najeriya a inda yake zaune, a wajen rantsar da sabbin ministoci da aka yi a fadar shugaban kasa Abuja.

Kara karanta wannan

An Bayyana Abun da Shugaban Kasa Tinubu Ya Fadawa Sabbin Ministoci 45 Da Aka Rantsar

A cikin bidiyon da Channels TV, ta wallafa a soshiyal midiya, an gano ministar wacce ta cika da farin ciki a duke a gaban shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu jim kadan bayan ta sa hannu a takardar daukar rantsuwar aiki.

Yayin taron, Ade-John ta sanya hannu a rijistan kama aiki, kafin ta karasa zuwa inda shugaban kasa Tinubu yake zaune sannan ta durkusa a gabansa, daga bisani ta yi musabaha da shi, rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan Najeriya sun yi martani yayin da ministar yawon bude ido ta durkusa a gaban Tinubu

Nan take bidiyon ya haddasa cece-kuce a dandalin X wacce aka fi sani da Twitter a baya.

Wani amfani da dandalin X Husseini Shaibu, Ph.D @igalaman ya rubuta:

"Ina kallon ministar yawon bude ido Lola Ade-John da na karafa Shuaibu Audu da kima saboda kan-kan da kansu kuma sun nuna girmamawa a wajen bikin rantsar da sabbin ministoci a fadar Villa.

Kara karanta wannan

An Aike da Muhimmin Sako Mai Jan Hankali Ga Shugaba Tinubu Kan Shari'ar Zaben Gwamnan Kano

"Na ji dadi! sosai."

Wani David Offor @DavidsOfforya rubuta:

"Ministar yawon bude ido, Lola Ade-John tana mai nuna cikakken girmamawa ga ubangidanta, Shugaban kasa Bula Ahmed Tinubu!!"

Kalli bidiyon a kasa:

An bayyana abun da Tinubu ya sanar da ministocinsa

A wani labarin kuma, mun ji cewa a kokarinsa na sake zaburar da gwamnatinsa mai watanni uku, Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake bayar da sabon umurni ga ministocin tarayyar Najeriya da aka rantsar.

A yayin bikin rantsar da ministocin a Abuja, a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta, Tinubu ya bukace su da su bayar da fifiko ga ra'ayin kasa da al'ummarta, sannan su yi watsi ga karkata ga yanki ko jiha daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng