Rikicin PDP: Makinde Da Sauran Yan G5 Sun Yi Gum Yayin da Wike Ya Kama Aikin Minista a Gwamnatin APC
- Tsoffin gwamnonin PDP da masu ci karkashin inuwar GS wanda Nyesom Wike ya jagoranta, basu taya tsohon gwamnan na jihar Ribas murnar samun mukamin minista ba
- A ranar Litinin, 21 ga watan Agusta ne aka rantsar da Wike a matsayin ministan Abuja karkashin gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu da APC
- Kafin nadinsa, Wike ya kasance gwamnan PDP sau biyu kuma ya yi adawa da dan takararsu na shugaban kasa a zaben 2023, Atiku Abubakar, saboda rikicin shugabanci a jam'iyyar adawar
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Ga dukkan alamu, kungiyar G5 na gwamnonin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da suka yi zanga-zanga gabannin zaben shugaban kasa na 2023 sun daina aiki bayan uku daga cikinsu sun fita daga harkokin siyasa bayan zaben.
Hakan ya kasance ne yayin da shugaban kungiyar, Nyesom Wike, wanda ya kasance gwamnan jihar Ribas a lokacin, ya zama ministan Abuja a karkashin gwamnatin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki sannan tawagar G5 suka yi gum.
Wike Ya Fasa Kwai, Ya Bayyana Cewa Gwamnonin PDP 10 Sun Gabatarwa Tinubu Da Sunaye Don Ba Su Mukamai
Yadda rikicin PDP ya sa Wike ya zama minista a gwamnatin APC
Jam'iyyar PDP ta yi fama da gagarumin rikici bayan Atiku Abubakar ya zama dan takararta na shugaban kasa sannan tsohon mataimakin shugaban kasar ya gaza shawo kan lamarin da hada kan jam'iyyar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wike, shugaban fusatattun gwamnonin PDP a wancan lokacin, sun janye goyon bayansu ga Atiku a babban zaben kuma jam'iyyar ta sha kaye.
Sabon ministan ya marawa Shugaban kasa Bola Tinubu baya a kan dan takarar jam'iyyarsa, Atiku, kuma yana ta ziyartan shugaban APC na kasa a baya-bayan nan.
Jerin gwamnonin G5 da basu taya Wike murna ba har yanzu
Sai dai kuma, baya ga Seyi Makinde na jihar Oyo, wanda ya yi nasarar komawa kan kujerarsa na gwamna a karo na biyu, sauran tsoffin gwmanonin G5 uku sune Samuel Ortom na Benue, Okezie Ikpeazu (Abia), Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu) wadanda suka rasa takararsu na son zama sanatoci.
Tun bayan nada Wike a matsayin minista, gwamnonin G5 sun yi tsit, basu taya takwaran nasu murna ba kuma ba su yi watsi da ci gaban ba.
Wike ya ce gwamnonin PDP sun aike Tinubu sunayen mutane
A wani labarin, mun ji cewa Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja, ya kira wadanda ke kira ga dakatar da shi daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a matsayin "yan rawan nanaye".
Wike, wanda ya rike mukamin gwamnan jihar Ribas sau biyu a karkashin jam'iyyar PDP ya yi martanin ne yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan rantsar da shi a matsayin minista a karkashin gwamnatin jam'iyyar APC a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta.
Asali: Legit.ng