“Zan Yi Aiki Kamar Magini”, Sabon Ministan Ilimi Tahir Mamman Ya Yi Bayani

“Zan Yi Aiki Kamar Magini”, Sabon Ministan Ilimi Tahir Mamman Ya Yi Bayani

  • Sabon ministan Tinubu, Farfesa Tahir Mamman, ya bayyana irin yadda zai gudanar da aiki a ofishinsa
  • Ya ce zai yi aiki tuƙuru kamar magini a shugabancin ma'aikatar ilimin da Shugaba Tinubu ya ba shi
  • Ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan karɓar rantsuwar fara aiki a fadar Gwamnatin Tarayya da ke Abuja

Abuja - Sabon ministan ilimi a gwamnatin Bola Tinubu, Farfesa Tahir Mamman, ya shiga ofis domin fara aiki kan muƙamin da Tinubu ya ba shi.

Mamman na cikin ministoci 45 da Shugaba Bola Tinubu ya rantsar a ranar Litinin, 21 ga watan Agustan 2023 a fadar shugaban ƙasa kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Tahir Mamman ya ce zai yi aiki tuƙuru
Farfesa Tahir Mamman ya ce zai yi aiki kamar magini a muƙamin ministan da Tinubu ya ba shi. Hoto: Tahir Mamman
Asali: Facebook

Ministan ya ce zai yi aiki kamar magini

Mamman wanda zai yi aiki tare da Yusuf Sununu daga jihar Kebbi a matsayin ƙaramin ministan ilimi, ya bayyana cewa zai yi aiki kamar magini.

Kara karanta wannan

"Ba Zan Yi Karya Domin Kare Gwamnatin Tinubu Ba" Sabon Minista Ya Yi Magana Mai Jan Hankali

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce burin magini a kullum shi ne ya ga ya jera bulullukan da aka jera ma sa domin ya yi gini da su, wanda a cikin wasu 'yan watanni sai a ga gida ya kammala.

Da yake jawabi a yayin da babban sakatare David Adejo ya tarbesa, Mamman ya ce ilimi shi ne ginshikin kowane ɓangare kuma shi ne tushen duk abinda za a yi domin ciyar da ƙasar gaba.

Ministan Tinubu ya faɗi dalilin da ya sa aka ba shi muƙami

Daya daga cikin ministocin da Shugaba Bola Tinubu ya rantsar a ranar Litinin, Dele Alake, ya bayyana dalilin da ya sa shugaban ya ba shi muƙamin da yake kai a yanzu.

Dele Alake ya ce Bola Ahmed Tinubu ya naɗa shi ministan ma'adinai ne saboda muhimmancin ma'aikatar a bangaren sabunta tattalin arziƙin ƙasa.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Yi Martani Bayan Tinubu Ya Rantsar Da Wike a Matsayin Ministan Abuja

Dele Alake ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan rantsar da shi a matsayin minista da Shugaba Tinubu ya yi a ranar Litinin a Abuja kamar yadda Vanguard ta wallafa.

Minista ya ce ba zai yi ƙarya don ya kare Tinubu ba

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan jawabin da ministan yaɗa labarai Muhammed Idris ya yi jim kaɗan bayan karɓar rantsuwar fara aiki.

Idris ya bayyana cewa ofishinsa ba zai riƙa yin ƙarya domin kare muradun gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng