Dele Alake Ya Ce Tinubu Ya Nada Shi Ministan Ma'adinai Ne Saboda Muhimmancin Ma'aikatar
- Dele Alake ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya naɗa shi minista ne saboda muhimmancin ma'aikatar
- Ya ce shi da kansa ya nemi Shugaba Bola Tinubu ya naɗa shi ministan bunƙasa ma'adinai saɓanin abinda ake tunani
- Ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan kammala rantsar da ministoci 45 da shugaban ƙasa ya yi a Abuja
Abuja - Ministan bunƙasa ma’adanai na ƙasa Dele Alake, ya ce shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ba shi mukamin ne saboda muhimmancin ma'aikatar a bangaren sabunta tattalin arziƙin ƙasa.
Alake ya bayyana hakan ne ga manema labarai jim kaɗan bayan ƙaddamar da ministoci 45 da Tinubu ya yi a ɗakin taron fadar shugaban ƙasa kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Dalilin Tinubu na bai wa Alake ma'aikatar ma'adinai
Dele Alake ya bayyana cewa shi da kansa ya nemi shugaba Tinubu ya naɗa shi ministan ma'adinai saɓanin abinda mutane suke zato.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya ce mutane da dama sun yi ta canke-canke a kansa tun a farko-farkon gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Ya bayyana cewa ma'aikatar bunƙasa ma'adinai ta ƙasa ma'aikata ce mai matuƙar muhimmanci a shirin da gwamnati take yi na sabunta tattalin arziƙin ƙasa.
Ina mutane suka yi hasashen za a tura Dele Alake
Dele Alake dai shi ne tsohon mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da ayyuka na musamman da tsare-tsare kamar yadda Daily Nigerian ta wallafa.
Jama'a da dama sun yi hasashen za a ba shi muƙamin ministan yaɗa labarai, sadarwa ko wata ma'aikatar mai alaƙa da wannan.
Sai dai muƙamin da Tinubu ya bai wa Alake a yanzu, ya kawo ƙarshen duk wasu hasashe-hasashe da jama'a ke yi a kansa.
"Najeriya Ba Zimbabwe Ba Ce": 'Yan Najerya Sun Yi Martani Mai Zafi Bayan An Bukaci Tinubu Ya Nada Dansa Minista
Tinubu ya sauyawa wasu ministocinsa muƙamansu
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan sauye-sauyen da Shugaba Bola Tinubu ya yi a cikin muƙaman ministocinsa da Majalisar Dattawa ta tabbatar.
A ranar Litinin, 21 ga watan Agustan da muke ciki ne dai Shugaba Tinubu ya rantsar da ministocin na sa domin su fara aiki.
Asali: Legit.ng