Jerin Manyan Ministoci 9 Da Ka Iya Bai Wa Shugaba Tinubu Kunya da Dalilai

Jerin Manyan Ministoci 9 Da Ka Iya Bai Wa Shugaba Tinubu Kunya da Dalilai

Shugaban kasa Bola Tinubu ya rantsar da ministocinsa guda 45 a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta, majalisa mafi girma a Afrika da kuma tarihin Najeriya tun bayan dawowar damokradiyya a 1999.

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

A makon jiya ne shugaban kasar ya rabawa ministocin ma'aikatu. Akalla tara daga cikinsu za su taka muhimmiyar rawa wajen fayyace nasara ko gazawar gwamnati mai ci a yanzu, da ayyukansu da ake sa ran zai yi tasiri kan yan Najeriya kai tsaye.

Shugaban kasa Buhari ya rantsar da ministocinsa
Wale Edun, Ali Pate Da Manyan Ministoci 7 Da Ka Iya Sa Tinubu Ya Gaza Da Dalili Hoto:Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Ministocin guda tara, duba ga yanayin aikinsu, basu da damar yin kura-kurai, sabanin sauran. Hakan ya kasance ne saboda ganin cewa kokarinsu ne zai tabbatar da ko Tinubu ya cika alkawaran da ya daukarwa yan Najeriya ta bangaren samar da ayyukan yi da rage talauci ko akasin haka.

Kara karanta wannan

'Tinubu Zai Tsamo Yan Najeriya Miliyan 70 Daga Kangin Talauci Cikin Watanni 6,’ Jigon APC

Ga cikakkun jerin ministocin a kasa:

Wale Edun

Ministan kudi kuma ministan da zai jagoranci tattalin arziki kai tsaye shine na farko a wannan jeri kasancewar shine zai tunkari kalubalen kudi da tattalin arzikin Najeriya a halin yanzu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Babban aikin da ke gabansa yayin da ya kama aiki a ranar Litinin, shine tabbatar da ganin cewar tallafin man fetur bai dawo ba da kuma tabbatar da ganin cewa Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fitar da dala da ake bukata domin daidaituwar kasuwar chanji.

Ali Pate Pate

Aikin Pate, ministan lafiya da walwalar jama'a, zai fayyace nasarar shugabancin Bola Tinubu kamar dai Edun.

Ana sa farfesan zai yi aiki tare da wasu ma'aikatu domin inganta rayuwar yan Najeriya.

Tahir Mamman

Farfesan bangaren shari'ar da aka nada a matsayin sabon ministan ilimi, zai yi tasiri sosai a rayuwar yan Najeriya saboda muhimmancin ma'aikatarsa ga mutanen kasar.

Kara karanta wannan

Sababbin Ministocin Najeriya da Aikace-Aikacen da Shugaban Kasa Tinubu ya ba su

An ce Najeriya ce hedikwata na inda ya fi yawan yara da ba sa zuwa makaranta a duniya.

Kasancewarsa shugaban jami'a mai zaman kanta a Abuja, ana sa ran Mamman zai kawo sauyi ga yadda matasan Najeriya ke tafiya karau a Turai da sauran yankunan duniya.

Doris Anite

Sabuwar ministar masana'antu, kasuwanci da saka hannun jari, wata minista ce da za ta taka muhimmiyar rawar gani wajen dawo da karfin gwiwar masu zuba jari a Najariya da farfado da ragin da aka samu a bangaren masu zuba jari a Najeriya daga waje.

Anite likita ce wacce ke da gogewa da kwarewa a bangaren hada-hadar kudi.

Adebayo Adelabu

Gyara wutar lantarki a Najeriya na iya sa shugaban kasa Tinubu ya zama gwani da ba a taba samun irinsa ba a kasar ta yammacin Afrika, kuma wannan ne dalilin da yasa Adelabu, sabon ministan wutar lantarki ke da muhimmiyar rawa da zai taka wajen tabbatar da nasararsa.

Kara karanta wannan

Meye zai faru? Shugaban matasan PDP ya bayyana kwarin gwiwar tsige Tinubu a mulki

Ma'aikatar wutar lantarki na Najeriya ta gurgunce, kuma wutar kasar ya ja baya sosai, yanzu haka ana fuskantar karancin kudi. Duk wadannan da sauransu sun sa shugaban kasa Tinubu na fuskantar matsin lamba.

Sauran ministoci hudu

Sauran ministocin da za su taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar sabuwar gwamnatin nan sune kamar haka:

David Umahi - Ministan ayyuka

Heineken Lokpobiri - Karamin ministan man fetur

Bosun Tijani - Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani

Abubakar Kyari - Ministan noma da tsaron abinci

Tinubu: "Ba Zamu Faɗi Karya Domin Kare Gwamnati Ba' Sabon Minista

A wani labarin, mun ji cewa sabon ministan yaɗa labarai da wayar da kan al'umma, Muhammed Idris, ya ce ma'aikatarsa ba zata yi wa 'yan Najeriya ƙarya domin kare gwamnati ba.

Ministan ya ce maimakon haka, "Zamu riƙa bayyana wa al'umma gaskiya a ko da yaushe."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng