Wike Ya Kama Aiki a Matsayin Ministan Abuja, Ya Ce Gine-gine Za Su Yo Ƙasa

Wike Ya Kama Aiki a Matsayin Ministan Abuja, Ya Ce Gine-gine Za Su Yo Ƙasa

  • Sabon ministan Birnin Tarayya Nysome Wike, ya yi jawabinsa na farko bayan soma aiki
  • Ya ce duk wasu gine-gine da aka yi su ba bisa ƙa'ida ba a cikin birnin, za su zuba ƙasa
  • Wike ya kuma bayyana cewa, za su ƙwace duk wasu filaye da suka daɗe ba tare da an gina su ba

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Ribas, kuma sabon ministan Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya kama aiki a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta.

Jim kaɗan bayan shigarsa ofis, ya bayyana cewa zai dawo da ainihin tsare-tsaren birnin na tarayya kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Wike ya ce gine-gine za su zubo ƙasa
Wike ya ce gine-gine da dama za su yo ƙasa. Hoto: Nyesom Ezenwo Wike
Asali: Facebook

Wike ya ce gine-gine za su yo ƙasa

Da yake jawabi bayan shigarsa ofis, Wike ya ce za su rushe duk wasu gine-gine da aka yi su ba a inda ya dace ba kamar yadda Daily Post ta wallafa.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Yi Martani Bayan Tinubu Ya Rantsar Da Wike a Matsayin Ministan Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

“Idan ka san ka yi gini a inda bai kamata a yi gini ba, to lallai fa zai yo ƙasa.”

Haka nan Wike ya kuma bayyana cewa duk wani da ya mallaki wani fili a cikin birnin kuma ya ƙi ginawa, zai iya rasa filin domin bai wa waɗanda suka shirya wuri su gina.

Ya ce ba za ta yi wu ba a bai wa mutum fili tuntuni, amma ya ƙi sayarwa masu shirin ginawa saboda yana jira ya yi tsada da yawa.

Wike ya ce ba zai ɗagawa kowa ƙafa ba

Nyesom Wike ya ci gaba da cewa duk wani gini da aka yi da ya saɓa da taswirar ginin Abuja, zai ci ƙasa ko mallakin wanene.

Ya ƙara da cewa duk wasu wurare da gwamnati ta ware domin shuke-shuke ko shaƙatawa da wasu suka yi gini a kansu, za a dawo da su yadda suke a da.

Kara karanta wannan

Matan zamani: Miji ya sha bulala saboda yiwa matarsa wani babban laifi, jama'a sun girgiza

Haka nan Wike ya tabbatarwa da masu yin cuwa-cuwa kan harkar filaye a birnin na Abuja, cewa abincinsu ya ƙare daga yanzu.

A ranar Litinin, 21 da ɗaya ne ga watan Agustan da muke cikin Nyesom Wike ya shiga ofis a matsayin sabon ministan Birnin Tarayya Abuja.

Wike ya ziyarci Ganduje a gidansa da ke Abuja

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan ziyarar da tsohon gwamnan Ribas, Nyesom Wike ya kai wa shugaban jam'iyyar APC ta ƙasa, Abdullahi Ganduje a gidansa da ke Abuja.

Ganduje ya bayyana cewa Wike ya ziyarce shi ne domin ya taya shi murnar zama shugaban APC na ƙasa da ya yi a kwanakin baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng