Tinubu Zai Rantsar Da Sabbin Ministocin Gwamnatinsa a Fadar Shugaban Kasa: Kai Tsaye
Hotuna da bidiyon sababbin Ministoci
Mai taimakawa shugaban Najeriya a kafofin zamani, ya fitar da hotuna da bidiyo bayan rantsar da ministocin.
Bayan tsohon Gwamnan Ribas, Nyesom Wike ya zama Minista, an gan shi ya na gaisawa da Shugaba Bola Tinubu.
An san ma'aikatar kowane Minista
Tsohon hadimin shugaban kasa, Tolu Ogunlesi ya ce wannan ne karo farko da wadanda ake rantsarwa za su san ma’aikatun da za su rike.
Hakan ya sabawa al’adar da aka gani a lokacin Ummaru Yar’adua, Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari tsakanin 2007 da 2023.
An rantsar da Ministoci
Aminiya ta ce Lateef Fagbemi ya nacikin wadanda aka fara rantsarwa a kujerar minister, shi ya zama babban lauyan gwamnatin tarayya.
A sahun farkon akwai matan da su ka samu shiga cikin gwamnatin Bola Tinubu irinsu Ekperipe Ekpo, Nkiruka Onyejeocha da Uju Kennedy.
Haka zalika an rantar da ministan ilmi, Farfesa Tahir Maman SAN da farko-farko.
Bayan nan sai aka rantsar da Sanata Abubakar Kyari a matsayin Ministan Noma da kuma Yusuf M. Tuggar da Ali Pate duka daga jihar Bauchi.
Farfesa Joseph Utsev da Sanata Heineken Lokpobiri sun yi rantsuwa a Aso Rock.