Atiku Ko Tinubu? Shugaban Matasan PDP Ya Bayyana Wanda Ya Kamata Kotun Zabe Ta Ba Nasara

Atiku Ko Tinubu? Shugaban Matasan PDP Ya Bayyana Wanda Ya Kamata Kotun Zabe Ta Ba Nasara

  • Muhammed Kadade, shugaban matasan jam'iyyar PDP na kasa, ya bukaci kotun zaben shugaban kasa da ta ayyana Atiku a matsayin wanda ya lashe zaben 2023
  • Kadade ya fadi hakan ne a cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Twitter, yana mai cewa hukuncin kotun zaben na da matukar muhimmanci ga makomar kasar
  • Jigon na PDP ya nuna karfin gwiwar cewa soke nasarar shugaban kasa Bola Tinubu ba zai haddasa tashin hankali ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Muhammed Kadade, shugaban matasan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya bukaci kotun zaben shugaban kasa da ta ayyana dan takarar jam'iyyarsa, Atiku Abubakar, a matsayin wanda ya lashe zaben 2023.

Kadade ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Juma'a, 18 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Cin Hanci: Abba Gida Gida Ya Tsorata, Ya Bukaci Binciken Gaggawa A Kotun Sauraran Korafe-Korafen Zabe

Jigon PDP ya ce kotun zabe ta ayyana Atiku Abubakar a matsayin wanda ya lashe zabe
Atiku Ko Tinubu? Shugaban Matasan PDP Ya Bayyana Wanda Ya Kamata Kotun Zabe Ta Ba Nasara Hoto: @atiku, @abba_kadade, @officialABAT
Asali: Twitter

Ya ce sama ba za ta fado ba idan kotun zaben ta soke nasarar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Shugaban kasa 2023: Atiku ne ya lashe zabe - Kadade ya yi ikirari

Shugaban matasan na PDP ya yi ikirarin cewa Atiku ne ainahin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana cewa hukuncin kotun zaben zai taka muhimmiyar rawar gani wajen yanke shawara ga makomar kasar.

Yayin da yake kokawa kan matsin tattalin arziki a kasar, shugaban matasan ya ce shugaban kasa Tinubu ya tabbatar da cewar shi sabon shiga ne a shugabanci da gwamnati.

Wani bangare na jawabinsa na cewa:

“Kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta kammala sauraren karar ta, kuma adalci shi ne babban abin da dan Adam ke bukata.
“Adalci na ba da dama ga sahihin shugabanci da jagoranci. Idan ba tare da adalci ba, al'amuran gwamnati za su lalace a cikin laifi. Tsarin adalcinmu ya kasance abu na karshe, wanda bayan shi makomar kasarmu zai kasance imma mai kyau ko ya tafi a banza."

Kara karanta wannan

Mukaman Ministoci: Yadda Shugaban Kasa Tinubu Ya Yi Watsi Da Keyamo, Ya Nada Kananan Ministoci 13

Jama'a sun yi martani

Ishaq Suleiman Junior ya ce:

"Gaba daya duniya na kallon kotun zaben, amma da izinin Allah, gaskiya za ta yi halinta imma suba Atiku nasara a zaben ko kuma mu sake zabe.
"Jagora na Allah yasa a gama lpia."

Atiku Princeya ce:

"JAGORA NA shine JAGORA a kodayaushe.✊Atiku na zuwa insha Allah!"

Tinubu ya amince a rabawa kowacce jiha kudin rage radadi

A wani labarin, mun ji cewa gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu ta amince a rabawa kowacce jiha ciki harda Abuja, tallafin naira biliyan 5, domin rage radadin cire tallafin man fetur.

Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno, ne ya tabbatar da hakan a ranar Alhamis, 17 ga watan Agusta, bayan taron majalisar tattalin arziki na kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng