Cin Amana: PDP Ta Shirya Tsaf Don Ladabtar Da Wike, Ortom, Makinde Da Saura
- Jam’iyyar PDP mai adawa ta riga ta shirya don dakatar da tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike daga jam’iyyar
- Wannan na zuwa ne bayan Shugaba Bola Tinubu ya nada Wike a matsayin ministan Abuja bayan majalisar Dattawa ta tantance shi
- Ana zargin Wike da sauran gwamnonin G5 da yi wa jam’iyyar zagon kasa tare da yi wa jam’iyyar APC mai mulki aiki a zabe
FCT, Abuja – Akwai yiyuwar jam’iyyar PDP ta latabtar da tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike da sauran gwamnonin G5.
Rahotanni sun tabbatar cewa jam’iyyar PDP na kokarin shawo kan dukkan matsalolin da jam’iyyar ta fada ciki, Legit.ng ta tattaro.
Daily Trust ta tattaro cewa PDP na dab da dakatar da shi ko kuma ta kore shi gaba daya daga jam’iyyar.
Meye PDP ta ce a kan Wike?
Wata majiya daga jam’iyyar ta ce:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“Jam’iyyar PDP na dab da dakatar da Wike ko kararshi gaba daya a jam’iyyar, su na jira ne kawai a rantsar da shi a matsayin minister.
“Jam’iyyar ta na son bin matakin cikin tsanaki saboda Wike ya na da mutane a jam’iyyar.”
Majiyar ta ce a kwanakin nan an gano Wike tare da shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Ganduje watakila ya na shirin koma wa jam’iyyar ce.
Wane mataki PDP za ta dauka a kan Wike?
Ta kara da cewa:
“Kun gan shi ya kai ziyara wurin Ganduje, shugaban APC, watakila ya na son sauya sheka zuwa APC ne ko kuma wannan abu zai sa a kore shi.
"Da zarar an rantsar da ministoci, ina mai ba da tabbaci PDP za ta dauki mataki.”
Majiyar ta ce PDP ba za ta lamunci yadda gwamnonin G5 su ke yi ba da sauran wadanda su ke biye wa Wike.
Tinubu Zai Rantsar Da Ministoci A Ranar Litinin
A wani labarin, Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a ranar Litinin zai rantsar da sabbin ministocin da ya nada a kwanakin baya, bayan majlisar Dattawa ta kammala tantance su.
Daga cikin sabbin ministocin akwai tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike wanda aka ba shi mukamin ministan Abuja.
Jam'iyyar PDP na zargin Wike da cin amana a lokacin zaben 2023 inda ya goyi bayan APC.
Asali: Legit.ng