Ganduje: APC Za Ta Hadiye Jam’iyyun Adawa a Karkashin Jagoranci Na
- Abdullahi Ganduje, ya yi magana kan shirin da suke yi wa jam'iyyun adawa a ƙarƙashin mulkinsa
- Ya ce jam'iyyun adawa da dama za su haɗe da jam'iyyar APC mai mulki kafin zaɓen 2027
- Ya bayyana hakan ne ranar Talata da ta gabata bayan ganawarsa da tsohon gwamnan jihar Filato
Abuja - Abdullahi Umar Ganduje, tsohon gwamnan jihar Kano, kuma shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, ya bayyana tsare-tsaren da yake yi wajen ganin jam'iyyun adawa sun haɗe da jam'iyya mai mulki.
Ganduje ya bayyana hakan ne ga manema labarai da yammacin ranar Talata, jim kaɗan bayan ganawarsa da tsohon gwamnan jihar Filato, Simon Lalong.
Gabanin wannan, Ganduje ya gana da tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike a gidansa da ke Abuja kamar yadda Nigerian Tribune ta wallafa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ganduje ya ce APC za ta hadiye jam'iyyun adawa
Ganduje ya bayyana cewa tuni ya fara tuntubar shugabannin jam'iyyun adawa domin ganin APC ta ƙara ƙarfi gabanin zaben 2027, inda ya ce yana ƙoƙarin jawo ƙarin mutane cikin jam'iyyar.
Ya ce tsare-tsaren da ya zo da su a yanzu, za su taimakawa jam'iyyar APC mai mulki sosai wajen samun nasara cikin sauki a zaɓen gaba, wato zaɓen 2027.
Ganduje ya kuma ce shiri ne suke yi ta ƙarƙashin ƙasa wajen ganin jam'iyyar ta ƙara riƙe 'ya'yanta da kuma ƙoƙarin ganin ta jawo 'yan jam'iyyun adawa domin su haɗe da ita.
Ganduje ya ce bai yi wa Wike tayin komawa APC ba
An tambayi Ganduje kan batun komawar tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike jam'iyyar APC, inda ya ce ba su tattauna hakan da shi ba kamar yadda Vanguard ta wallafa.
Mataimakin Gwamnan Jihar Arewa Ya Bayyana Adadin Mutanen Da Ta'addanci Ya Raba Da Muhallansu a Jiharsa
Ya bayyana cewa Wike ya zo wurinsa ne domin taya shi murnar zama shugaban jam'iyya da ya yi, a yayinda shi kuma ya taya shi murnar zama minista da ya yi a gwamnatin Bola Tinubu.
Ya kuma ce sun tattauna da Wike kan yadda zai yi aiki tuƙuru wajen ganin ya ciyar da ma'aikatar da aka ba shi gaba, amma ba su tattauna batun komawarsa APC ba.
An gargaɗi Tinubu kan yin watsi da El-Rufai
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan kiran da Osita Okechukwu, wanda yana daga cikin jiga-jigan da suka kafa jam'iyyar APC ya yi wa Shugaba Tinubu dangane da El-Rufai.
Ya gargadi Tinubu kan yunƙurin cire Malam Nasir El-Rufai daga cikin ministocinsa, duba da irin amfanin da zai yi wa jam'iyyar a zaɓen 2027 idan Allah ya kaimu.
Asali: Legit.ng