Shettima Na Jagorantar Taron NEC Kan Rabon Kayan Tallafi Ga 'Yan Kasa

Shettima Na Jagorantar Taron NEC Kan Rabon Kayan Tallafi Ga 'Yan Kasa

  • Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, yana jagorantar taron NEC a fadar Gwamnatin Tarayya
  • Ana sa ran taron zai mayar da hankali kan rabon kayan tallafi don ragewa 'yan ƙasa raɗaɗi
  • Za kuma a tattauna batutuwa masu muhimmanci da suka shafi tattalin arziƙin ƙasa a wajen taron

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Fadar Gwamnatin Tarayya Abuja - Kashim Shettima kamar yadda rahotanni suka nuna, a yanzu haka yana ganawa da 'yan majalisar ƙoli ta tattalin arziƙin ƙasa (NEC), a Abuja.

Zaman ya samu halartar gwamnoni 36 na Najeriya, da wasu daga cikin ministoci da suka haɗa da na FCT, na kuɗi da kuma gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).

Haka nan a wajen taron akwai shugaban kamfanin mai na Najeriya, da kuma ƙarin wasu mambobi kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Shettima na jagorantar taron NEC
Shettima yana jagorantar taron majalisar ƙoli ta tattalin arziƙin ƙasa (NEC). Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

An Gurfanar Da Matashi Gaban Kuliya Bisa Zargin Tafka Ta'asa a Makabarta a Legas

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Abubuwan da za a tattauna a taron NEC da Shettima ke jagoranta

A wajen taron NEC na yau, ana sa ran za a tattauna batutuwan da suka shafi halin da lalitar Gwamnatin Tarayya ke ciki da kuma sauran ƙarin matsalolin da suka shafi ƙasa.

Sai dai abu mafi muhimmanci da majalisar tattalin arziƙin za ta tattauna akai shi ne yadda za a gabatar da rabon kayan tallafi da za a bai wa 'yan Najeriya.

Za a ba da kayayyakin tallafin ne saboda ragewa 'yan ƙasa raɗaɗin da cire tallafin man fetur da gwamnatin Tinubu ta yi ya jefa su a ciki.

Wannan dai shi ne taron NEC na uku tun bayan hawan gwamnatin Tinubu kamar yadda The Cable ta wallafa.

Gwamnonin da suka halarci taron NEC na yau

Kara karanta wannan

Masanin Tattalin Arziƙi Ya Fadi Abinda Zai Faru Idan Ministocin Tinubu Suka Fara Aiki

Daga cikin gwamnonin da suka halarci taron akwai Abdulrahman Abdulrazak na Kwara, Hope Uzodinma na Imo, Inuwa Yahya na Gombe, Dauda Lawal na Zamfara, Dakta Alex Otti na Abia, Babajide Sanwo-Olu na Legas da kuma Ademola Adeleke na jihar Osun.

Ƙarin gwamnonin su ne Sanata Bala Mohammed na Bauchi, Sanata Uba Sani na Kaduna, Sheriff Obrevwori na Delta, Farfesa Charles Soludo na Anambra, Godwin Obaseki na Edo, Yahaya Bello na Kogi, da Umaru Namadi na jihar Jigawa.

Haka nan a wajen taron akwai Umo Eno na Akwa Ibom, Prince Bassey Otu na Kuros Riba, Lucky Aiyedatiwa na Ondo, Dapo Abiodun na Ogun, Ahmad Aliu na Sokoto, Agbu Kefas na Taraba, Abdullahi Sule na Nasarawa, Peter Mbah na Enugu, da Farfesa Babagana Zulum na Borno.

Gwamnonin jihohin Katsina, Ribas, Yobe, Adamawa, Kano, da Kebbi ba su samu halarta ba, inda suka turo mataimakansu a madadinsu.

Kashim Shettima ya fadi amfanin cire tallafin mai

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Babban Malamin Addini Ya Fadawa Tinubu Abinda Zai Faru Idan Bai Yi Maganin Halin Da Ake Ciki Ba

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan amfanin cire tallafin man fetur da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya bayyana.

A wani taron ƙarawa juna sani na Hukumar Sauyin Yanayi ta ƙasa(NCCC), Shettima ya bayyana cewa daga cikin alfanun cire tallafin akwai kare lafiyar al'umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng