Shugaban Kasa Tinubu Zai Rantsar Da Ministocinsa a Ranar Litinin, Akume

Shugaban Kasa Tinubu Zai Rantsar Da Ministocinsa a Ranar Litinin, Akume

  • Fadar shugaban kasa ta bakin babban sakataren gwamnatin tarayya ta sanar da rana da lokacin da shugaban kasa Bola Tinubu zai rantsar da ministocinsa
  • A ranar Laraba, 16 ga watan Agusta ne aka rarrabawa kowani minista aikin da zai yi a majalisar Tinubu
  • SGF, Dr George Akume, ya bayyana cewa za a rantsar da ministocin a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta da karfe 10:00 na safe

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai rantsar da sabbin ministocinsa a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta, a cibiyar taro na fadar shugaban kasa, Abuja da misalin karfe 10:00 na safe.

Babban sakatern gwamnatin tarayya, Dr George Akume, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Laraba, 16 ga watan Agusta, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

An Bayyana Lokacin Da Shugaba Tinubu Zai Rantsar Da Ministocinsa Domin Fara Aiki

Tinubu zai rantsar da ministoci ranar Litinin
Shugaban Kasa Tinubu Zai Rantsar Da Ministocinsa a Ranar Litinin, Akume Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Kowani minista zai zo da mutum biyu, SGF

TVC ta rahoto cewa a cikin sanarwar dauke da sa hannun Mista Willie Bassey, daraktan labarai na ofishin babban sakataren tarayya, Akume ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ana sa ran masu girma ministoci da za a rantsar su zo da mutum biyu kowannensu. Gaba daya masu girma ministoci da bakin da aka gayyata su zama a zaune da misalin karfe 9:00 na safe."

Legit.ng ta rahoto a baya cewa shugaban kasar ya rabawa ministocin da majalisar dattawa ta tantance aiki a ranar Laraba.

An bai wa tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ministan babban birnin tarayya, sannan Festus Keyamo ministan sufurin jiragen sama.

Shehu Sani ya yi martani kan wanda Tinubu ya nada ministan tsaro

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa tsohon sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya nuna damuwarsa matuka yayin da shugaban kasa Bola Tinubu ya nada Muhammad Badaru, tsohon gwamnan jihar Jigawa a matsayin ministan tsaro.

Kara karanta wannan

A Karshe, Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Shugaban Jam’iyyar Labour Party Na Kasa

Haka kuma, Tinubu ya nada tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle a matsayin karamin ministan tsaro a ranar Laraba, 16 ga wata Agusta.

Sani a cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter a daren Laraba, ya yi mamaki kan dalilin da yasa ba a nada tsohon soja a matsayin ministan tsaro ba yayin da Najeriya ke fuskantar matsalolin tsaro a yanzu haka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng