“Zai Karfafa Jam’iyyarmu”: Ganduje Ya Magantu a Kan Shirin Sauya Shekar Wike Daga PDP Zuwa APC
- Shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya bayyana abun da zai faru idan tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya koma APC mai mulki
- Ganduje ya bayyana cewa sauya shekar Wike zuwa APC zai karfafa damammakin da jam'iyyar ke da shi a babban zaben 2027
- Tsohon gwamnan na jihar Kano ya bayyana cewa jam'iyyar mai mulki za ta fito da sabon tsari don kara yawan mabiyanta
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Jawabin shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Dr. Abdullahi Ganduje na baya-bayan nan ya kara karfafa rade-radin da ake yi na zargin sauya shekar tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.
"Karin jam'iyyu za su yi maja a cikin APC", cewar Ganduje bayan ganawa da Wike
Wannan ya kasance ne yayin da Ganduje ya bugi kirgin cewa jam'iyyar za ta kara karfi, cewa ana kan tattaunawa domin samun wasu jam'iyyun adawa da za su yi maja a APC, rahoton Vanguard.
Ganduje ya yi wannan hasashen ne a ranar Laraba, 16 ga watan Agusta, yayin da yake karin haske a kan ziyarar da zababben minista kuma tsohon gwamnan jihar Ribas ya kai masa a ranar Talata, 15 ga watan Agusta, rahoton The Nation.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Da aka tambaye shi kan ko Wike zai koma APC a matsayinsa na minista a gwamnatin APC karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Tinubu, Ganduje ya ce tsohon gwamnan na Ribas ya shirya ba jam'iyya mai mulki hadin kai ba tare da lallai sai ya koma tafiyar ba.
An bayyana lokacin da Tinubu zai rantsar da ministocinsa
A gefe guda, mun ji cewa shugaban ƙasa Bola yana duba yiwuwar rantsar da majalisar ministocinsa a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta, kusan wata uku bayan an rantsar da shi a kujerar shugabancin ƙasar nan.
A cewar rahoton The Guardian, wani majiya a fadar shugaban ƙasa ne ya bayyana hakan, inya ya ƙara da cewa Shugaba Tinubu na iya rantsar da ministocinsa 45 da majalisar dattawa ta amince da su.
Jan ƙafar da shugaba Tinubu ya yi wajen zaɓo ministocinsa ya sanya wasu ƴan Najeriya sun fara dawowa daga rakiyar tafiyarsa, inda suka daina yabawa da kamun ludayin salon mulkinsa.
Asali: Legit.ng