Primate Ayodele Ya Yi Hasashen “Mummunan Al’amari” Kan Godswill Akpabio, Orji Kalu Da Sauransu

Primate Ayodele Ya Yi Hasashen “Mummunan Al’amari” Kan Godswill Akpabio, Orji Kalu Da Sauransu

  • Malamin addini kuma shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Babatunde Elijah Ayodele, ya aika gagarumin gargadi ga yan majalisar Najeriya
  • An shawarci yan majalisar wakilai da sanatoci da su yi abun da ya dace a mazabunsu mabanbanta
  • 'Yin abun da ya kamata', acewar Primate Ayodele, zai hana tashin hankali a kan zababbun jami'an gwamnati

Abuja - Primate Elijah Ayodele, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, ya ce ya hango ana yi wa yan majalisar wakilai da sanatoci jifa da duwatsu dare da ihun ba ma yi.

Saboda haka, malamin addinin ya shawarci yan majalisa da su zamo masu lura da addu'a domin dakile "wannan mummunan al'amari".

Primate Ayodele ya gargadi yan majalisa
Primate Ayodele Ya Yi Hasashen “Mummunan Al’amari” Kan Godswill Akpabio, Orji Kalu Da Sauransu Hoto: @primate_ayodele, @SPNigeria
Asali: Twitter

"Ana iya jifan Sanatoci", Primate Ayodele

Primate Ayodele ya kuma shawarci shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio; Orji Uzor Kalu, sanata mai wakiltan Abia ta arewa, da takwarorinsu da su yi abun da ya kamata a mazabunsu mabanbanta.

Kara karanta wannan

Ministocin Tinubu: Mutum 5 Da Suka Sha Wahala Kafin a Tantance Su a Majalisa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Primate Ayodele ya yi hasashen ne a cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Twitter a daren ranar Asabar, 12 ga watan Agusta.

Ya ce:

“Mu dage da addu’a sosai don kada su fara jifan wasu Sanatocinmu, ‘yan Majalisar Wakilai, kuma mutane su rika zaginsu, suna kai musu hari.
"Mu yi addu'a, su zuba ido. Ina shawartan yan siyasa da su yi duk abun da ya kamata a wannan gabar."

SERAP Za Ta Shigar Kara Kan Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio

A wani labari na daban, mun ji cewa kungiyar SERAP ta sanar da cewa za ta shigar da ƙara kan shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, bisa kalaman da ya yi na biyan kuɗin shaƙatawa ga sanatoci.

A lokacin zaman majalisar na ranar Laraba, 9 ga watan Agusta, Akpabio ya bayyana cewa an tura wa sanatocin kuɗi domin su ji daɗin hutun su, amma daga baya ya janye kalamansa inda ya ce addu'o'i aka tura musu.

Kalaman na Akpabio ya janyo ƴan Najeriya sun yi ta caccakarsa a soshiyal midiya, waɗanda suka yi ƙorafin cewa ƴan majalisar na ta bushasha da kuɗi a daidai lokacin da ƴan Najeriya ke ci gaba da shan wahala a sakamakon cire tallafin man fetur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng