Shugabannin APC Da Dama Sun Yi Murabus Daga Kujerunsu a Jihar Neja
- Yan kwanaki bayan murabus din shugaban APC a jihar Neja, wasu karin jami'an jam'iyya mai mulki sun sauka daga kujerunsu
- A baya-bayan nan, Sakataren jam'iyyar, Barista Khaleel Ibrahim Aliyu da mataimakin shugaban jam'iyyar, Abdulsalam Madaki sun ajiye mukaminsu
- Jam'iyyar APC ta jaddada cewar babu wani rikicin cikin gida da ya dabaibayeta kamar yadda ake hasashe
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Niger - Yan kwanaki bayan shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Neja, Haliru Zakari Jikantoro, ya yi murabus daga kujerarsa, wasu karin mutum biyu sun ajiye mukamansu a jam'iyyar mai mulki.
Sakataren jam'iyyar, Barista Khaleel Ibrahim Aliyu da mataimakin shugaban jam'iyyar, Abdulsalam Madaki sun yi murabus.
Dalilin su na sauka daga mukamansu
Sai dai sun bayyana cewa matakin da suka dauka bai da alaka da rikicin da ya kunno kai a jam'iyyar tun bayan zabar Mohammed Idris Malagi a matsayin minista, jaridar Daily Trust ta rahoto.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Amma wasu 'ya'yan jam'iyyar sun ce murabus din da suka yi umurni ne daga sama domin gwamnan bai aminta da shugabancin jam'iyyar a jihar ba tun bayan zaben fidda gwanin gwamna na 2022.
Karin jami'an APC za su yi murabus, majiyoyi
Majiyoyi sun ce akwai karin jami'an APC da za su yi murabus a kwanaki masu zuwa domin ba masu biyayya ga gwamnan damar jan ragamar harkokin jam'iyyar a jihar.
Da aka tuntube shi, sakataren labarai na jam'iyyar, Musa D. Sarkinkaji, ya fada ma Daily Trust cewa jam'iyyar bata fuskantar rikicin cikin gida kamar yadda mutane ke hasashe.
Ya ce jami'an jam'iyyar uku sun yi murabus ne da kansu domin gudanar da wasu harkokin.
Shugaban APC a jihar Neja ya yi murabus daga kujerarsa
A baya Legit.ng ta rahoto cewa shugaban jam'iyyar APC a jihar Neja, Haliru Zakari Jikantoro, ya yi murabus daga kan kujerarsa.
Kamar yadda rahotanni suka kawo, Jikantoro ya yanke shawarar sauka daga mukaminsa ne a bainar jama'a ba tare da bayyana wani dalili ba.
Hakan na zuwa ne bayan wata ganawa da kwamitin aiki na jam'iyyar a jihar suka yi a sakatariyar APC da ke garin Minna, a gaban babban mai ba gwamnan jihar shawara kan harkokin siyasa, Alhaji Mohammed Nma Kolo.
Asali: Legit.ng