Hankalin Gwamna Obaseki Na Edo Ya Tashi Kan Zargin Yunkurin Yi Ma Sa juyin Mulki

Hankalin Gwamna Obaseki Na Edo Ya Tashi Kan Zargin Yunkurin Yi Ma Sa juyin Mulki

  • Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo, ya zargi mataimakinsa Philip Shaibu da shirya ma sa juyin mulki domin ya ɗare kujerarsa
  • Obaseki ya bayyana hakan ne a yayin da yake ganawa da 'ya'yan jam'iyyar PDP masu biyayya na jihar
  • Gwamnan ya ce ya fahimci hakan ne a lokacin zaɓen kakakin majalisar jihar, inda Shaibu ya goyi bayan wani daban

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Benin City, jihar Edo - Jam'iyyar PDP a jihar Edo ta shiga cakwakiya a yayinda gwamnan jihar Godwin Obaseki, ya yi zargin cewa mataimakinsa Philip Shaibu na shirya maƙarƙashiyar kifar da gwamnatinsa.

Obaseki ya bayyana hakan ne a wani ɗan gajeren bidiyo da aka wallafa a shafin gidan talabijin na AIT na X (Twitter a da).

Gwamnan Edo ya zargi mataimakinsa da shirya masa tuggu
Gwamnan Edo ya zargi mataimakinsa da yunkurin yi ma sa juyin mulki. Hoto: Godwin Obaseki
Asali: Twitter

Yadda mataimakina ya yi yunƙurin min juyin mulki, Obaseki ya yi bayani

Kara karanta wannan

An Bayyana Abin da Sanatoci Suka Gayawa Shugaba Tinubu Kan Fafata Yaki Da Jamhuriyar Nijar

Godwin Obaseki ya bayyana cewa jim kaɗan bayan kammala zaɓen 2023 ne ya gana da Shaibu, inda ya yi ma sa maganar zaɓen gwamna na jihar da ke ƙaratowa da kuma buƙatar ƙarfafa jam'iyyar PDP a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce daga nan ba su ƙara wata magana makamanciyar ta ba sai dai ji ya yi an ce mataimakin na sa na tuntuɓar 'yan jam'iyya.

Ya ƙara da cewa lokacin da aka gudanar da zaɓen kakakin majalisar jihar, Shaibu ya haɗa kai da 'yan jam'iyyar APC, inda suka zaɓi wani ɗan takarar daban da wanda gwamnan yake so.

A kalaman Obaseki:

“Idon mataimakin gwamnan ya rufe wajen ganin ya karɓi mulki, ta yadda zai iya yin komai, ciki har da shirya juyin mulki ga gwamnansa."

Ga bidiyon a ƙasa:

Motar Obaseki ta maƙale saboda mamakon ruwan sama a Benin City

Kara karanta wannan

Shugaban Kwaddibuwa Ya Ayyana Sojojin Nijar a Matsayin 'Yan Ta'adda, Ya Fadi Abinda Ya Kamata a Yi Mu Su

Wani bidiyo da ya yaɗu a Intanet wanda Legit.ng ta yi rahoto a kansa, ya nuna yadda ɗaya daga cikin motocin ayarin gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ta maƙale a kan titi sakamakon ruwan sama a Benin City.

Waɗanda suka ɗauki bidiyon kuma suka yaɗa shi sun nuna jin daɗinsu da ya zamto shi ma gwamnan ya fuskanci irin abinda talakawa suka daɗe suna fuskanta.

Oshiomole ya ce naira 30,000 ta yi kaɗan a matsayin albashi

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan iƙirarin da tsohon gwamnan jihar Edo Adams Aliyu Oshiomole ya yi, na cewa naira 30,000 ta yi kaɗan a matsayin mafi ƙarancin albashi.

Oshiomole ya ce ko mai yi ma sa shara a gida yana ba ta abinda bai gaza naira 60,000 ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng