An Samu Rikici Tsakanin APC Da PDP Kan Batun Kwamishinoni a Jihar Kwara
- An samu wata 'yar hayaniya tsakanin 'yan Majalisar Dokokin jihar Kwara
- Rikicin dai ya faru ne kan jerin sunayen kwamishinoni da gwamnan jihar ya turo majalisar
- 'Yan PDP sun yi zargin cewa an ɗage zaman majalisar ne saboda rashin turo sunayen kwamishinonin kamar yadda gwamnan ya yi iƙirari
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Ilorin, jihar Kwara - An samu hayaniya tsakanin 'yan majalisun jiha na jam'iyyar APC, da kuma na jam'iyyar PDP kan sunayen kwamishinonin jihar da majalisar za ta tantance.
Babban sakataren yaɗa labarai na kakakin majalisar, Shehu AbdulKadir Yusuf ya bayyana cewa, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya aikawa majalisar sunayen waɗanda zai naɗa kwamishinoni.
Abinda ya janyo rikici tsakanin PDP da APC a kwara
Abdulkadir ya ce gwamnan ya turo sunayen mutane 20 ne da yake so ya ba muƙaman kwamishinoni a gaban majalisar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Haka nan ya ce gwamnan ya haɗo da ƙarin wasu mutane 10 da yake so ya naɗa masu ba shi shawara na musamman a bangarori daban-daban.
Sai dai majalisar ta sanar da ɗage zamanta domin tantance kwamishinonin, wanda hakan bai yi wa 'yan jam'iyyar PDP daɗi ba.
Martanin jam'iyyar PDP kan kwamishinonin
Da take mayar da martani kan lamarin, jam'iyya PDP ta hannun sakataren yaɗa labaranta Prince Tunji Morounfoye, ya bayyana jerin sunayen kwamishinonin da aka ce an miƙa ga majalisar a matsayin yaudara.
Ya ce kundin tsarin mulki ya tanadi cewa dole ne gwamna ya miƙa sunayen kwamishinoninsa cikin 60 ko ƙasa da haka.
Tunji ya yi zargin cewa babu wasu sunaye ma da gwamnan ya turawa majalisar domin a tantancesu a matsayin kwamishinoni.
Sai dai wani rahoto da jaridar Leadership ta wallafa, ya nuna cewa gwamnan na jihar Kwara ya aika da sunayen kwamishinoninsa tun makonni biyu da suka gabata.
Gwamnan Kwara ya amince a bai wa kowane dalibi naira 10,000
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan naira 10,000 da gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq ya amince a bai wa ɗaliban manyan makarantu a jihar.
Gwamnan dai ya ɗauki wannan matakin ne domin ragewa ɗaliban jihar raɗaɗin da suke ciki na cire tallafin man fetur da aka yi.
Asali: Legit.ng