Dalilin Da Yasa Buhari Ya Fi Son Mamora Ba Osinbajo Ba a Matsayin Mataimakinsa, Boss Mustapha Ya Magantu
- Boss Mustapha ya fallasa wani sirrin boye game da wanda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buharis ya fi so a matayin abokin takara
- Tsohon sakataren gwamnatin tarayyan ya bayyana cewa Sanata Adeleke Olurunnimbe Mamora shine wanda Buhari ya so a matsayin mataimaki ba Yemi Osinbajo ba
- Sai dai kuma, Mustapha bai bayyana ko a lokacin zaben shugaban kasa na 2015 ko 2019 bane
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya yi bayani kan wanda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya so ya zama abokin takararsa.
Buhari ya so Mamora, ne ba Osinbajo ba, inji Boss Mustapha
Yayin da Mustapha bai bayyana ko a lokacin zaben shugaban kasa na 2015 ko 2019 bane, ya bayyana cewa Buhari ya so Sanata Adeleke Olurunnimbe Mamora ne zai zama abokin takararsa ba tsohon mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ba.
Tsohon sakataren gwamnatin tarayyar ya bayyana hakan ne yayin taron cin abincin dare na 'godiya' da Mista Akinbode Oluwafemi ya jagoranci shiryawa a Abuja, jaridar The Guardian ta rahoto.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Mustapha ya bayyana cewa Mamora na daya daga cikin mambobin majalisar zartarwa da Buhari ke dauka da muhimmanci.
Sai dai, bai bayyana ko Buhari ya so Mamora ya zama mataimakinsa ne gabannin wa'adin mulkinsa na farko ko kafin zaben 2015 lokacin da aka ce Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, jagoran jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a wancan lokacin ya zabi tsohon mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo don takara tare da Buhari, rahoton Premium Times.
Almajiran Shiekh Dahiru Bauchi sun nemi Tinubu ya hana El-Rufai mukamin minista
A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto a baya cewa gamayyar kungiyar masu karatu da haddar Al-Qur'ani sun yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da kada ya rantsar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a matsayin minista domin gaskiya, adalci, zaman lafiya da dorewar kasar.
Daraktan kula da harkokin ilimi a wata Gidauniya ta Sheikh Dahiru Bauchi wanda ya yi jawabi ga manema labarai a Bauchi a madadin malaman, Sheikh Sidi Aliyu Sise, ya bukaci Tinubu da ya yi taka-tsan-tsan sannan kada ya rantsar da azzaluman yan siyasa.
Asali: Legit.ng