Mataimakin shugaban kasa, Osinbajo ya cilla kasar waje ziyarar aiki

Mataimakin shugaban kasa, Osinbajo ya cilla kasar waje ziyarar aiki

  • Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya cilla kasar Tanzaniya don wata ziyarar aiki
  • Rahotanni sun bayyana cewa, mataimakin shugaban zai sauka ne a Arusha na kasar ta Tanzaniya
  • Hakazalika, an kuma ce, zai karbi bakuncin takwaransa na kasar ta Tanzaniya, Philip Mpango

Abuja - Ana sa ran mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo zai bar Abuja a ranar Alhamis, 2 ga watan Satumba zuwa Arusha, yankin Arewa maso gabashin kasar Tanzaniya.

Laolu Akande, babban mataimaki na musamman ga Osinbajo kan harkokin yada labarai, ya bayyana hakan a wani takaitaccen bayani a Abuja, The Nation ta ruwaito.

Da dumi-dumi: Mataimakin shugaban kasa, Osinbajo ya cilla kasar waje
Matamakin shugaban kasa | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: Facebook

Akande ya kara da cewa takwaransa na Tanzaniya, Philip Mpango zai karbi bakuncinsa a Arusha, kuma ana sa ran zai dawo Najeriya ranar Litinin, 6 ga watan Satumba, in ji Vanguard.

Kara karanta wannan

Buhari ya kori ministocinsa: Martani da shawarin 'yan Najeriya ga shugaban kasa

A wani bangare na aikin da zai kaishi, Osinbajo zai ziyarci Kotun Adalci da Kare Hakkokin Dan Adam ta Afirka (ACJHR), wata hukuma ta Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) a Arusha.

Buhari ya bayyana dalilin da ya sa ya kori ministocinsa biyu

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana dalilin da yasa ya sallami ministoci biyu daga cikin yan fadarsa da ya zaba a ranar 21 ga watan Agustan 2019.

Sanarwar da kakakin shugaban kasar, Femi Adesina ya fitar ta ce bukatar 'sabon jini' ne yasa aka yi sauyin ministocin kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Legit.ng ta ruwaito cewa an sallami Muhammad Sabo Nanono, Ministan Noma da Raya Karkara da Sale Mamman, Ministan Makamashi.

An maye gurbin su da Dr Mohammed Mahmood Abubakar, Ministan Muhalali da Abubakar D. Aliyu, Karamin Ministan Ayyuka da Gidaje.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya sabunta naɗin magatakardan hukumar TRCN

Har wa yau, sanarwar ta ce sauyin ministocin wani abu ne da 'za a cigaba da yi' idan bukatar hakan ta taso.

Buhari ya kori ministocinsa: Martani da shawarin 'yan Najeriya ga shugaban kasa

A bangare guda, a wani abin da ya zama abin mamaki ga 'yan Najeriya da yawa ya kuma girgiza su, Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Laraba, 1 ga Satumba ya sallami wasu ministocinsa biyu daga aiki.

A cikin shekaru hudun farko da yayi akan mulki tsakanin shekarar 2015 zuwa 2019, shugaban ya rike dukkan membobin majalisarsa hannu bibbiyu har zuwa karshen wa'adin mulkinsa na farko.

Mutane da yawa na ganin membobin majalisar Buhari za su ci gaba da kasancewa a mukamansu har zuwa shekakar 2023 lokacin da Buhari zai bar ofis a matsayin shugaban Tarayyar Najeriya.

Sai dai, lamari ya sha bambam, yayin da shugaban, ta hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai da yada labarai, Femi Adesina, ya sanar da korar ministan wutar lantarki, Engr. Sale Mamman da na ma’aikatar noma da raya karkara, Mohammed Sabo Nanono.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Buhari ya bayyana dalilin da ya sa ya kori ministocinsa biyu

Asali: Legit.ng

Online view pixel